Ban san komai ba - Kanwar Maina ta nisanta kanta da asusun banki da aka alakanta da yayanta

Ban san komai ba - Kanwar Maina ta nisanta kanta da asusun banki da aka alakanta da yayanta

Misis Nafisat Aliyu, kanwar Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban hukumar fansho, a ranar Laraba, 15 ga watan Janairu ta nesanta kanta da wani asusun banki da aka bude da sunanta.

Ta yi magana ne a gaban Justis Okon Abang na babbar kotun tarayya, Abuja.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa asusun mai lamba: 4510002792, a daya daga cikin bankunan zamani na kasar, na da nasaba da Maina, wanda a yanzu yake fuskantar tuhume-tuhume 12 kan zambar kudi.

NAN ta kuma ruwaito cewa a ranar 25 ga watan Oktoba 2019, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta gurfanar da Maina tare da dansa Faisal a gaban kotu da kuma kamfaninsa na Common Input Property and Investment Limited.

Koda dai an gurfanar da Faisal kan tuhume-tuhume uku da ke da nasaba da zambar kudi, daga uban har dan basu amsa tuhumar da ake masu ba.

Nafisa ta fada ma kotu cewa bata san yadda aka bude asusun ba.

Ya ce Toyin Meseke, ma’aikacin banki, ya kasance mai hats a gidansu da ke Karu, Abuja kuma abokin kaninta Khalid.

“Su kan zo gidana cin abinci a lokacin,” in ji ta.

Nafisat ta ce Toyin ya zo gidanta wasu yan shekarun baya sannan ya bukaci takardar Nepa nata, inda ta kara da cewa bayan shekaru uku zuwa hudu, sai ta fara samun sakonni.

Shaidar ta bayyana cewa ta tunkare shi sannan ta tambayi dalilin da yasa take samun sakonnin bankin.

“Na yi barazanar zuwa ofishinsa na tayar da rigima, idan bai yi wani abu a kai ba. Sai ya bani hakuri cewa zai yi wani abu a kai.

“Ban yi tunanin cewa ko babu lamba, Toyin na iya yin abunda zai yi ba tare da lamba na ba.

“Daga baya ne sai EFCC suka kana yar’uwata Fatima a Kaduna.

“Don haka, sai na kai kaina ofishin EFCC, saboda an fada mani cewa shakka babu Za su bibiye ni.

KU KARANTA KUMA: Hukuncin kotun koli: Buba Galadima ya yi hasashen abunda ka iya zama makomar Ganduje

“Don haka, sai na zauna na yi masu bayanin lamarin a lokacin da suka tambaye ni ko nasan wani abu game da asusun,” in ji ta.

Nafisa ta ce adireshi, lambar waya da sa hannun ya da ke kai duk na bogi ne, cewa fasfot da hotonta ne kadai na gaskiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel