Karamin yaro dan Fulani makiyayi ya gamu da ajalinsa a hannun miyagu a Kaduna

Karamin yaro dan Fulani makiyayi ya gamu da ajalinsa a hannun miyagu a Kaduna

Wani yaro mai shekaru 15 a duniya dan Fulani mai kiwon shanu ya gamu da sharrin miyagu a lardin Kukum dake cikin masarautar Kagaro na karamar hukumar Kaura a jahar Kaduna, inda suka kashe shi yayin da yake kan hanyarsa ta komawa gida.

Da yake zantawa da jaridar Daily Trust, shugaban al’ummar Fulani na masarautar Kagoro, Ardon Fada Alhaji Isa Ori ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 5 na yammacin Litinin a lokacin da wasu matasa suka tare yaron tare da sauran yan uwansa.

KU KARANTA: Badakalar naira biliyan 2: Kanwar Abdulrashid Maina ta sake tsunduma shi cikin matsala

“Da muka ga bamu ga daya daga cikin yaranmu bane sai muka fita muna nemansa, a haka muka gano gawar Abdulkadir a bakin ruwa a Hayin Rafi a Kukum. Bamu dade da masa jana’iza ba tare da shugaban karamar hukuma, Katuka Bege Ayuba da wakilin DPO na Yansanda.” Inji shi.

Shi ma shugaban kungiyar Miyetti Allah na karamar hukumar Kaura, Salisu Ibrahim Hari ya bayyana damuwarsa da aukuwar lamarin, sa’annan ya yi kira ga fulanin yankin da su cigaba da zama lafiya, musamman tun jami’an tsaro sun fara aikin kamo masu laifin.

Haka zalika, shugaban hukumar, Bege Katuka ya nemi makiyayan kada su dauki doka a hannunsu: “Na yi alkawari zan shawo kan matsalar tsaron dake damunmu, zamu yi bincike domin gano musabbabin mutuwarsa da kuma kama wadanda suka aikata hakan.

“Kamar yadda ka sani, a bakin rafi aka gano gawarsa, muna jiran rahoton binciken likitoci don sanin ko kashe shi aka yi ko kuwa nutsewa ya yi cikin ruwa.” Inji shi.

A wani labarin kuma, wasu gungun yan bindiga sun kaddamar da farmaki a kauyen Makosa dake cikin karamar hukumar Zurmi na jahar Zamfara inda suka halaka jami’an kiwon lafiya guda biyu dake aiki sa ido a allurar riga kafin cutar shan inna da ake yi a kauyen.

Wasu shaidun gani da ido sun bayyana cewa yan bindigan sun dira karamin asibitin ne dauke da muggan makamai inda suke bindige jami’an kiwon lafiyan bayan wata cacar baki da ta kaure a tsakaninsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng