Mahaifiyarshi ta sayar da gidanta don ganin yayi karatu, yanzu ya matukin jirgin sama mafi kankanta a Ingila

Mahaifiyarshi ta sayar da gidanta don ganin yayi karatu, yanzu ya matukin jirgin sama mafi kankanta a Ingila

- Seth Veen Beek matashi ne mai shekaru 18 da ya kafa tarihin zama matukin jirgin sama mafi karancin shekaru a duniya

- Ya sadaukar da nasarar shi ga mahaifiyar shi wacce ta siyar da gidanta don biya mishi kudin makaranta

- Ya karba lasisin zama matukin jirgin sama na haya inda ya zama dalibi mafi kwazo a makarantar su a kasar Girka

Bayan siyar da gidan gado da mahaifiyar shi tayi don yayi karatu, Seth Van Beek ya karba lasisin shi a matsayin matukin jirgin sama na haya wanda yayi karatun a kasar Girka.

Kamar yadda jaridar Metro UK ta wallafa, saurayin mai shekaru 18 ya samu lasisin ne bayan horarwar watanni 18 da ya samu kuma ya fito da sakamako mai matukar kyau.

Ya sadaukar da nasarar shi ga mahaifiyar shi mai shekaru 42 'yar kasar Zimbabwe. Frances ta siyar da gidanta mai dakunan bacci uku inda ta koma mai daki biyu don ta samu kudin biyawa danta karatun da zaiyi.

Matashin wanda ya nuna matukar hazakar shi, yace ya nemi nasara ne don yasa mahaifiyar shi alfahari dashi.

KU KARANTA: Tirkashi: Daliba ta dauki bidiyon lakcara da yace zai kayar da ita matukar bata bari yayi lalata da ita ba

Yace: "Akwai bukatar mutane su bibiyi burinsu kuma nayi sa'a da na cika nawa saboda mahaifiyata tayi alfahari dani. Babu abinda zan iya ba tare da taimakonta ba."

Frances tace: "Ban samu ingantaccen ilimi ba saboda haka ne na dinga kokarin ganin Seth ya samu karatu mai kyau. Tuntuni nake sanar da shi cewa in dai yana son abin a ranshi toh tabbas zai iya samu. Tunanin shine matukin jirgi a UK mafi karancin shekaru na sanya ni farin ciki."

Matashin ya fara fatan zama matukin jirgi ne tun yana da shekaru 8 a duniya bayan mahaifiyar shi ta kai shi hutu don ya ga duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel