Tirkashi: Daliba ta dauki bidiyon lakcara da yace zai kayar da ita matukar bata bari yayi lalata da ita ba

Tirkashi: Daliba ta dauki bidiyon lakcara da yace zai kayar da ita matukar bata bari yayi lalata da ita ba

- Wani malami a jami'ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife ya shiga tashin hankali bayan wata daliba ta nadi sautin muryar shi yana nemanta da lalata

- Malamin ya kada ta kwas din shi a lokacin tana aji uku kuma ya ce mata ba zata ci ba ko a yanzu matukar bata bashi hadin kai ba

- Bayan kai shi kara da tayi gaban kwamitin ladabtarwar makarantar, wasu daliban sun bayyana a matsayin shaida don kuwa sunce ya nemesu a baya

Olabisi Olaleye malami ne a jami'ar Obafemi Awolowi dake Ile-Ife wanda ake zargin shi da neman lalata da wata daliba mai suna Mutunrayo Afolayan. Malamin yayi wa Afolayan barazanar cewa zata cigaba da faduwa matukar bata bashi hadin kai ba.

Dalibar ta tunkari wani abokin aikin lakcaran wanda yace ba zai iya zuwa yi mishi magana ba. Dalibar ta bayyana cewa ta fadi kwas din a lokacin da take aji uku kuma yayi mata barazanar kayar da ita matukar bata bashi hadin kai ba.

Dalibar ta nadi sautin muryar malamin a yayin da taje ofishin shi yana shafa jikinta tare da yi mata maganganun rashin kamun kai. A nan ne ya bayyana barazanar gareta wacce duk ta nade a wayarta.

Dalibar ta tunkari wasu malamai a fannin karatun shari'a a makarantar inda suka bata shawarar kai kara ga hukumar makarantar.

KU KARANTA: Shugabar karamar hukuma ta rabawa matasa baro su dinga haya suna kai mata kudi

Jin yadda lamarin ya faru yasa Olaleye ya hanzarta sakin mata sakamakon waccan jarabawar da tayi wanda ke bayyana ta ci.

Kwamitin ladabtarwa ta makaranta ya mika takardar neman karin bayani ga Olaleye amma ya musanta wannan zargin, lamarin da yasa aka kira shi gaban kwamitin tare da lakcaran da ta fara kaiwa kokenta.

Lakcaran da ta fara kaiwa koken yace a 2014 ya taba samun Olaleye a kan wata daliba da yake nema da lalata, amma sai ya tozarta shi tare da bukatar ya bar mishi ofishin shi.

An kira dalibar gaban kwamitin wacce ta bada shaidar sautin muryar tare da wasu dalibai mata da suka tabbatar da cewa ya nemi su a baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng