Shugabar karamar hukuma ta rabawa matasa baro su dinga haya suna kai mata kudi

Shugabar karamar hukuma ta rabawa matasa baro su dinga haya suna kai mata kudi

- Shugabar karamar hukumar Nsukka ta jihar Enugu ta raba baruka ga matasa a matsayin hanyar fatattakar talauci

- Shugabar karamar hukumar an bata jagorancin jihar ne na rikon kwarya a watan Disamba kafin a yi zabe a watan Fabrairu

- Barukan da ta raba wa matasan, ta basu ne a matsayin haya don hana su zaman kashe wando

Shugaban kwamitin riko kwarya na karamar hukumar Nsukka dake jihar Enugu, Chinwe Ugwu ta jawo wa kanta maganganu daban-daban a kafafen sada zumuntar zamani bayan hotunanta tana tallafawa matasa wajen yakar talauci, ta hanyar raba musu baro ya bazu a tuwita a ranar Litinin.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, Ugwu ta raba wa matasa baro ne a karamar hukumarta na haya a matsayin hanyar samar musu da abin yi a maimakon zaman banza.

An yi taron raba baron ne a dakin taron matasa dake karamar hukumar Nsukka a jihar Enugu.

KU KARANTA: Buhari dabbobi ya kamata yaje ya dinga mulka ba mutane ba - Deji Adeyanju

An zabi shugabar karamar hukumar ne don ta rike kujerar tun a watan Disamba da ta gabata kafin a yi zaben da aka saka ranarsa a watan Fabrairu.

Wani ma'abocin amfani da tuwita wanda shine ya wallafa hotunan ya rubuta: "Shugabar karamar hukumar Nsukka a jihar Enugu wacce Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi ya zaba don rikon kwarya ta raba barukan haya ga jama'ar karamar hukumar Nsukka ta jihar. Jihar Enugu dai na a hannun Ubangiji."

Wasu ma'abota amfani da tuwita din sun garzaya sashin tsokaci inda suka yi wa shugabar kaca-kaca.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel