Gungun miyagu yan bindiga sun kai hari asibitin Zamfara, sun kashe ma’aikatan 2

Gungun miyagu yan bindiga sun kai hari asibitin Zamfara, sun kashe ma’aikatan 2

Wasu gungun yan bindiga sun kaddamar da farmaki a kauyen Makosa dake cikin karamar hukumar Zurmi na jahar Zamfara inda suka halaka jami’an kiwon lafiya guda biyu dake aiki sa ido a allurar riga kafin cutar shan inna da ake yi a kauyen.

Premium Times ta ruwaito wasu shaidun gani da ido sun bayyana cewa yan bindigan sun dira karamin asibitin ne dauke da muggan makamai inda suke bindige jami’an kiwon lafiyan bayan wata cacar baki da ta kaure a tsakaninsu.

KU KARANTA: Fadar shugaban kasa ta gargadi duk gwamnonin dake bindiga da kudaden kananan hukumomi

Mazauna garin sun bayyana sunayen ma’aikatan biyu kamar haka; Lawali Suleiman da Aliyu Muhammad, sai kuma wani mutum daya da ya samu rauni a sanadiyyar bude wutan da suka yi, amma a yanzu haka yana samun kulawa a wani asibiti na daban.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa yan bindigan sun yi ma mazauna yankin fashi, musamman ma matan dake kan layi domin a yi ma yaransu allurar, inda suka kwace musu kudade da wayoyinsu.

Ita ma rundunar Sojan kasa ta tabbatar da aukuwar harin cikin wani takarda da ta fitar inda tace: “Da misalin karfe 2:30 na rana yan bindiga dauke da AK 47 sun kai farmaki wani asibiti a kauyen Makosa zikin karamar hukumar Zurmi.

“A yayin harin sun kashe mutane biyu, Aliyu Muhammad da Lawali Suleiman, sa’annan mutane biyu sun samu rauni daga harbin bindiga. Bincike ya nuna sun kwashe dukkanin dabbobin dake kauyen inda suka tsallaka dasu zuwa mafakarsu da bata wuce kilomita 1 daga kauyen ba, ruwa ne ya raba su.” Inji takardar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel