Gwamnatin jahar Katsina ta sanya dokar takaita sana’ar acaba a Katsina

Gwamnatin jahar Katsina ta sanya dokar takaita sana’ar acaba a Katsina

Gwamnan jahar Katsina, Malam Aminu Bello Masari ya rattafa hannu kan wata sabuwar dokar hana zirga zirga acaba a garuruwan jahar Katsina gaba daya tun daga karfe 7 na dare zuwa karfe 6 na safiya.

Katsina Post ta ruwaito babban lauyan gwamnatin jahar Katsina, kuma kwamishinan shari’a na jahar, Ahmed El-Marzuk ne ya sanar da haka jim kadan bayan gwamnan ya rattafa hannunsa a kan sabuwar dokar.

KU KARANTA: Fadar shugaban kasa ta gargadi duk gwamnonin dake bindiga da kudaden kananan hukumomi

Sai dai majiyar Legit.ng ta bayyana cewa samar da wannan sabuwar doka baya rasa nasaba da matsalolin tsaro da ake fuskanta a jahar Katsina, musamman na yan bindiga da kuma masu garkuwa da mutane.

Kwamishina El-Marzuk ya bayyana cewa dokar za ta fara aiki ne daga ranar 20 ga watan Janairun shekarar 2020, sai dai yace dokar ba za ta yi aiki a kan jami’an hukumomin tsaro ba da suka hada da Sojoji, Yansanda, Civil Defense, kwastam, NDLEA da sauransu.

Kwamishinan ya kara da cewa gwamnatin jahar ta dauki wannan mataki ne saboda ta gano cewa yawancin hare haren da ake kaiwa da kuma satar mutane da ake yi a Katsina ana yin su ne da babura da Keke Napep.

Daga karshe kwamishinan ya sanar da cewa dokar ta tanadi hukuncin daurin shekara 1 ga duk wanda aka kama ya karya ta, sa’annan ya nemi jama’a dasu baiwa gwamnati hadin kai da sauran hukumomin tsaro domin dabbaka wannan doka.

A wani labarin kuma, wasu gungun yan bindiga sun kaddamar da farmaki a kauyen Makosa dake cikin karamar hukumar Zurmi na jahar Zamfara inda suka halaka jami’an kiwon lafiya guda biyu dake aiki sa ido a allurar riga kafin cutar shan inna da ake yi a kauyen.

Wasu shaidun gani da ido sun bayyana cewa yan bindigan sun dira karamin asibitin ne dauke da muggan makamai inda suke bindige jami’an kiwon lafiyan bayan wata cacar baki da ta kaure a tsakaninsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng