Fadar shugaban kasa ta gargadi duk gwamnonin dake bindiga da kudaden kananan hukumomi
Fadar shugaban kasar Najeriya ta gargadi gwamnoni dake bindiga da kudaden kananan hukumomin su da su kauce ma yin hakan ko kuma su sha mamaki idan wa’adin mulkinsu ya kare, tunda a wannan loakcin basu da sauran kariya.
Babban mashawarcin shugaban kasa Buhari a kan harkar Neja Delta, Sanata Ita Enang ne ya bayyana haka ta bakin mai magana da yawunsa, Edet Ekpeyong Etuk, inda yace Sanatan ya bayyana haka ne yayin hira a gidan rediyon tarayya.
KU KARANTA: Gobara ta tashi a dakin ajiyar gawa na babban asibitin gwamnatin tarayya Gusau
Sanatan ya yi kira ga babban akantan kasa da babban lauyan gwamnati da su sanya idanu a kan kudaden da ake tura ma gwamnatocin jahohi domin su ceto kananan hukumomi daga mawuyacin halin da suke ciki.
“Ya kamata gwamnonin su sani, cewa zasu fuskanci tuhuma bisa dokokin Najeriya bayan an cire musu rigar kariya. A yanzu haka ciyayin sun mamaye yawancin ofisoshin kananan hukumomin, sa’annan asibitocin su basa aiki, sai dai malaman jinya su dinga karban albashi daga gida basa aikin komai.
“Gwamnoni sun ci mutuncin kananan hukumomi, sun musu daurin demon minti, tare da goyon bayan majalisun dokokin jahohi, babu ta yadda shuwagabannin kananan hukumomin suka iya, duk da cewa kotun koli ta kwatar musu yancin su.” Inji shi.
A wani labarin kuma, gwamnan jahar Neja, Abubakar Sani Bello ya bayyana cewa daga watan Janairun shekarar 2020 gwamnatin za ta fara biyan ma’aikatan jahar sabon karancin albashi na naira 30,000.
Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Laraba, 15 ga watan Janairu yayin da yake ganawa da manema labaru bayan ya karbi bakuncin kafatanin shuwagabannin kananan hukumomin jahar guda 25 da suka kai masa ziyarar goyon baya.
Ciyamomin su 25 sun kai ma Gwamna Abubakar ziyara a fadar gwamnatin jahar Neja ne domin taya shi murnar nasarar daya samu a gaban kotun koli bisa kararsa da jam’iyyar PDP da dan takararta a zaben gwamna na 2019 suka shigar da shi suna kalubalantar sakamakon zaben.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng