An sake samun wata jaha a Arewa da za ta biya sabon karancin albashin N30,000

An sake samun wata jaha a Arewa da za ta biya sabon karancin albashin N30,000

Gwamnan jahar Neja, Abubakar Sani Bello ya bayyana cewa daga watan Janairun shekarar 2020 gwamnatin za ta fara biyan ma’aikatan jahar sabon karancin albashi na naira 30,000.

Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Laraba, 15 ga watan Janairu yayin da yake ganawa da manema labaru bayan ya karbi bakuncin kafatanin shuwagabannin kananan hukumomin jahar guda 25 da suka kai masa ziyarar goyon baya.

KU KARANTA: Duniya ina za ki da mu? Matashi ya lakada ma mahaifiyarsa dan banzan duka a jahar Ebonyi

Ciyamomin su 25 sun kai ma Gwamna Abubakar ziyara a fadar gwamnatin jahar Neja ne domin taya shi murnar nasarar daya samu a gaban kotun koli bisa kararsa da jam’iyyar PDP da dan takararta a zaben gwamna na 2019 suka shigar da shi suna kalubalantar sakamakon zaben.

Gwamnan ya tabbatar da cewa tuni ya kafa kwamiti da zai kula da wannan bukata ta ma’aikata, kuma tattaunawa yayi nisa domin lalubo tsarin da ya kamata a bi wajen fara aiwatar da dokar sabuwar albashin.

“A yanzu babban abin da muka sanya a gaba shi ne yadda zamu magance matsalar wadanda dokar sabon karancin albashin ya shafa kai tsaye, ma’ana ma’aikatan dake amsan albashin da bai wuce N30,000 ba.

“Na bayar da umarnin a fara biyan albashin daga karshen wannan watar, ta yadda wadanda suka cancanta ko kuma suke karbar abin bai wuce sabon albashin ba za su fara gani a kwaryarsu. Amma wadanda suke amsan albashin da ya wuce N30000 kuma sai a rukuni na gaba.” Inji shi.

Sai dai gwamnan ya koka inda yake cewa a halin da ake ciki a yanzu, kashi 80 na kudaden dake shigo ma gwamnatin jahar Neja suna tafiya ne wajen biyan albashi, ya kara da cewa a jahar dake da ma’aikata 27,000 da al’umma miliyan 4, yana shan wahala wajen biyan albashi da kuma gudanar da manyan ayyuka.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel