Tirkashi: Boka ya dirkawa matar fasto cikin shege

Tirkashi: Boka ya dirkawa matar fasto cikin shege

- Kamar a wasan kwaikwayo dai aka kama boka da dirkawa matar fasto ciki

- Faston da matar shi suna neman haihuwa ne ido rufe kafin matar ta yanke shawarar kaiwa bokan kukanta

- Bokan ne shugaban bokayen yankin kuma shugaban wajen bautar gargajiya wanda shaharar shi ta sa manyan 'yan kasuwa ke ziyartar shi

Kamar dai a wasan kwaikwayo lamarin ya faru. Wani boka mai suna Ekwe-baba ne ake zargi da dirkawa matar fasto ciki bayan shekarun da ta dauka bata haihuwa.

Wani mutum mai suna Agholor Abraham ne ya wallafa labarin a kafar sada zumuntar zamani. A lokacin da ake wannan rubutun, ba a gano yankin da lamarin ya faru ba.

Kamar yadda Agholor ya ruwaito, rashin haihuwa ce ta sa matar faston ta tunkari bokan don neman mafita. Taji labarin irin yadda yake shawo kan ire-iren matsalolin nan ba bata lokaci. An gano cewa boka da matar fasto sun fada son juna, lamarin da ya kaishi dirka mata ciki.

KU KARANTA: Kilu ta ja bau: Wani ya kashe miji a yayin da yake kokarin raba fada tsakanin ma'aurata

Kamar yadda Agholor Abraham ya rubuta: "Matar fasto ta samu juna biyu a watannin biyu da suka gabata kuma cikin na boka ne. Bokan ne babba a wajen bautar gargajiya dake yankin. Dan asalin Ughelli ne kuma ana kiran shi da Ekwe-Baba. Manyan 'yan kasuwa na zuwa neman sa'a wajen shi amma ba a san cewa ya fara soyayya da matar fasto ba.

"Kowa ya sani, faston da matar shi na neman haihuwa ido rufe amma shiru. Matar ta yanke shawarar zuwa wajen bokan ne ko zasu dace. Sai kuwa tayi sa'ar samun ciki amma ba da mijinta ba. Tuni mutane suka fara zarginta maita tare da shawartar faston da ya sake ta."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel