Tashin hankali: Dan damfara ya kone budurwarsa kurmus kan zargin cin amana

Tashin hankali: Dan damfara ya kone budurwarsa kurmus kan zargin cin amana

- Alkali ya bukaci a adana mishi wani matashi dan damfarar yanar gizo a gidan yari dake Ikoyi

- Victor Oji mai shekaru 18 ya bankawa budurwar shi mai shekaru 24 wuta bayan da ya zargeta da cin amana

- Wannan laifin yaci karo da tanadin dokokin laifukan jihar Legas sashi na 223

Alkali ya bukaci a adana Wani matashi mai shekaru 18 kuma dan damfarar yanar gizo a gidan yari na Ikoyi a jihar Legas. Ana zargin Victor Oji ne da laifin bankawa budurwar shi wuta wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwarta a Iba cikin birnin Ojo dake Legas.

Alkali A Kusanu bata saurari rokon matashin ba amma ta bukaci a adana shi a gidan yari har zuwa lokacin da zata samu shawara daga daraktan gurfanarwa na jihar. Ta dage sauraron karar zuwa 19 ga watan Fabrairu.

Tun farko dai, dan sanda mai gurfanarwa, Jimah Iseghede ya sanar da kotun cewa a ranar 7 ga watan Disamba 2019 wajen karfe 10 na safe ne wanda ake zargin ya aikata laifin kisan kai.

KU KARANTA: Asirin wata budurwa ya tonu da take amfani da jinin al'adarta tana dafawa saurayinta abinci

Yace wanda ake zargin ya bankawa budurwar shi mai suna Tolani Mariam mai shekaru 24 wuta sakamakon zarginta da yake da cin amana.

Kamar yadda mai gurfanarwa ya bayyana, budurwar tace zata ziyarci 'yar uwarta ne amma sai ta dawo bayan kwanaki.

Iseghede yace wanda ake zargin ya ga bidiyon budurwar shi a otal tana shan miyagun kwayoyi, lamarin da ya jawo aika-aikar da yayi.

Wannan laifin kuwa yaci karo da sashi na 223 na dokokin laifukan jihar Legas na 2015 kuma hukuncin hakan kisa ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel