Mai ilimin kimiyya a Japan ya Musulunta saboda wata ayar Qur'ani (guda daya)

Mai ilimin kimiyya a Japan ya Musulunta saboda wata ayar Qur'ani (guda daya)

Mafi yawanci lokuta za a ji masu bijirewa addini suna kafa hujja da kimiyya tare da bayyana cewa ita ce mafita ba addinai ba.

Sai dai, fitaccen mai ilimin kimiyya a kasar Japan, Dakta Okuda, ya sha banban da masu irin wancan tunani bayan ya rungumi addinin Musulunci tare da bayyana cewa ba zai iya rayuwa ba sai a kan tafarkin Mahalicci.

A cewar Dakta Okuda, rayuwarsa ta kasance marar ma'ana da tarbiya kafin ya karbi addinin Islama.

"Gaskiya rayuwata ta kasance marar tsafta, kuma a cikin duhu, saboda ban san gaskiya ba a wancan lokacin," a cewarsa.

Ya bayyana cewa, ya shiga neman gaskiya a cikin addinai bayan mallaki dumbin ilimin kimiyya har zuwa lokacin da ya zo kan addinin Islama, kuma ya tsaya ya nazarce shi.

Dakta Okuda ya bayyana cewa batun hukunci a tsarin Musulunci shine ya fara jan hankalinsa kafin daga bisani ya ci karo da wata aya data canja rayuwarsa a wurin wani taron kara wa juna ilimi.

Mai ilimin kimiyya a Japan ya Musulunta saboda wata ayar Qur'ani (guda daya)
Dakta Okuda
Asali: Twitter

Ayar data ja hankalin Dakta Okuda ita ce daya daga cikin ayoyin sura ta15, aya ta 26 inda Allah yake cewa, "kuma mun halicci mutum ne daga tabo (kasa mai danko)".

DUBA WANNAN: Matashi ya kone budurwarsa kurmus saboda zargin cin amana

A yayin da ya cigaba da neman ilimin addinin Islama, Dakta Okuda ya yi hijira zuwa birnin Aleppo na kasar Syria inda har ya koyi yaren Larabci.

Dakta Okuda ya bayyana cewa ya samu kwanciyaar hankali da karin natsuwa bayan shigarsa addinin Musulunci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng