Matashi ya kone budurwarsa kurmus saboda zargin cin amana

Matashi ya kone budurwarsa kurmus saboda zargin cin amana

Wani matashi mai shekaru 18 da ake zargin cewa dan damfara ne ta hanyar yanar gizo ya kone budurwarsa kurmus a garin Iba dake karamar hukumar Ojo a jihar Legas.

A ranar Talata ne aka gurfanar da matashin mai suna Victor Oji a gaban wata kotun majistare dake yankin Ebute Meta, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito.

Alkaliyar kotun, Uwargida A. Kusanu, ta bayar da umarnin a tsare matashin a gidan ajiya dake Ikoyi har zuwa ranar 19 ga watan Fabrairu, lokacin da kotun zata sake zama bayan tuntubar darektan sashen gurfanar da jama'a na jihar Legas.

Kafin hakan, dan sanda mai gabatar da kara, Insifekta Jimah Iseghede, ya fada wa kotun cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne da misalin karfe 10:00 na safiyar ranar 7 ga watan Disamba, 2019, a garin Iba.

Ya shaida wa kotun cewa Matashin ya kone budurwarsa, Toni Mariam, mai shekaru 24, bisa zargin cewa tana cin amanarsa.

Iseghede ya kara da cewa, lamarin ya faru ne bayan Marigayiyar ta sanar da Matashin cewa zata ziyarci 'yar uwarat da ta haihu, amma bai kara ganinta ba sai bayan wasu kwanaki.

A cewar Iseghede, Matashin ya kashe budurwarsa tasa ne bayan ganinta a cikin faifan bidiyo tare da wasu Maza suna shan miyagun kwayoyi a wani Otal.

Dansandan ya bayyana cewa, laifin matashin ya saba da sashe na 223 na kundin aikata manyan laifuka da hukunce - hukuncensu da jihar Legas ta zartar a shekarar 2015.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel