Wanda bai ji bari ba: Yan bindigan Katsina sun nemi Sojojin Najeriya su tsagaita wuta

Wanda bai ji bari ba: Yan bindigan Katsina sun nemi Sojojin Najeriya su tsagaita wuta

Kungiyoyin miyagu yan bindiga dake cikin dazukan jahar Katsina sun nemi dakarun Soji su zauna dasu domin sulhuntawa sakamakon ruwan masifa da Sojojin suka sauke musu a cikin dazukan.

Jaridar Katsinapost ta ruwaito rundunar Sojin Najeriya ta 8 ce take jagorantar hare haren da Sojojin suke kai ma yan bindigan a cikin daji, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dimbin yan bindiga tare da sabbaba jagororinsu neman sauki.

KU KARANTA: Sarkin yawa: Manyan kasashen duniya 5 sun fara tattaun matakin da zasu dauka a kan Iran

Yan bindigan sun aika sakon neman sulhu da zaman lafiyar ne ga babban kwamandan rundunar ta 8 dake garin Gusau a jahar Zamfara, ta hannun yan aike, inda suka jaddada shirinsu na rungumar zaman lafiya tare da duk wani sharadi da za’a shimfida musu.

Sai dai rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa za ta cigaba da gudanar da aikinta na kwace duk makaman dake hannun yan bindigan kafin ta duba yiwuwar shiga tattaunawar zaman lafiya da yan bindigan.

A wani labarin kuma, wasu gungun yan bindiga dadi sun kai ma jami’an rundunar Yansandan Najeriya hari a jahar Delta a yayin da suke aikin binciken motoci a shingen binciken ababen hawa dake cikin garin Asaba, babban birnin jahar Delta.

Wannan lamari ya auku ne da misalin karfe 9 na dare a kasuwar Abraka dake cikin garin Asaba, inda yan bindigan suka jikkata Yansanda guda uku, sa’annan suka kwashe bindigoginsu guda uku.

A yanzu haka Yansanda sun can a cikin mawuyacin hali a wani asibiti da ba’a bayyana sunansa ba suna samun kulawa. Wasu ganau ba jiyau ba sun tabbatar da cewa yan bindigan sun yi amfani da adda wajen kakkafta ma Yansandan sara.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel