Ganduje zai hana aurar da yara mata har sai sun kammala makarantar sakandare

Ganduje zai hana aurar da yara mata har sai sun kammala makarantar sakandare

- Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Abdullahi Ganduje, ta bayyana sabbin dokokin ilimi a jihar

- Sabuwar dokar da aka yi don shawo kan matsalar auren wuri ga yara mata, ta tabbatar da cewa dole ne yara mata su kammala sakandire kafin ayi musu aure

- Wadannan sabbin dokokin kuwa sun fara shawo kan matsalar auren wuri a jihar, wacce itace ta daya a wannan bangaren a fadin Najeriya

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa sabbin dokokin ilimi a jihar sun rage yawan aurar da yara kanana a jihar. Gwamnan ya sanar da hakan ne a daren Lahadi a wani taron kare hakkin dan Adam wanda hukumar kare hakkin dan Adam ta kasa, NHRC ta shirya.

Gwamnan, wanda ya kasance daya daga cikin wadanda suka karba kambun girmamawa, yace an hade tsarin tsangaya da na ilimin zamani a jihar. Yayi bayanin cewa gwamnatin shi ta kirkiro ilimin firamare da sakandire kyauta a jihar tare da duban yaran da suka bar makaranta don tabbatar da sun koma.

KU KARANTA: Abin mamaki: An ruwan damina na farko a jihar Legas

Kamar yadda yace, "Mun hada tsarin tsangaya da na ilimin zamani a yanzu. Hana ilimin yara mata tare da yi musu auren wuri duk mun kawar dashi. A dokar yanzu, dole yarinya mace ta kammala sakandire kafin ayi mata aure."

A Arewacin Najeriya, jihar Kano ce ke da mafi yawan kaso na auren wuri ga yara mata. Ba Arewacin Najeriya kadai ba, har a Najeriya baki daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng