Miji ya yiwa matarshi dukan tsiya saboda kawai yana so ya burge abokanan shi

Miji ya yiwa matarshi dukan tsiya saboda kawai yana so ya burge abokanan shi

- Wani magidanci na fuskantar hukuncin shekaru 16 a gidan yari bayan da ya kashe matar shi

- Anastasia mai shekaru 28 ta sha mugun duka ne a hannun mijinta har tayi sumar da bata farka ba sai mutuwa

- Bayan dukanta tare da mugayen raunika, yayi bidiyonta kuma ya tura wa abokan shi don tabbatar musu da cewa yana iya juya matar shi

Wani magidanci na fuskantar hukuncin shekaru 16 a gidan yari bayan da yayi wa matar shi mugun duka har ta suma. Bayan dukan da yayi mata, ya dau bidiyo wanda ya tura wa abokan shi don tabbatar da ya isa da gidan shi.

Yayi mata duka babu kakkautawa bayan da ta sanar dashi cewa zata bar shi. Hotuna daga wannan mummunan lamarin sun bayyana matar a kan katifa tare da raunika daban-daban a jikinta.

Bayan da aka kai Anastasia mai shekaru 28 asibiti, an ga raunika tare da karyayyun kasusuwa a jikinta. Anastasia Ovsiannikova tace ga garinku bayan kwanaki shida da faruwar lamarin. Ta yanke shawarar barin mijinta mai suna Maxim Gribanov wanda ke juyata son ran shi ciki har da sanya ta barin aikinta. Tayi doguwar suman da bata tashi bane tun bayan mugun dukan da ta sha.

KU KARANTA: Rikicin Boko Haram: Zulum ya bawa sojoji da 'yan sanda motoci guda 70 na aiki

"Mace mai cike da burika amma ya datseta. Ya halaka ta har lahira. Ya kamata a yi mishi yadda yayi mata. Gribanov ya dinga dukanta ne na sa'o'i masu yawa kuma ya nuna wa abokan shi bidiyon." Kawar Anastasia ta sanar.

Anastasia tayi yunkurin barin mijinta mai cin zarafinta ne bayan da ta hadu da wata kawa wacce ta bata kwarin guiwa. Duk da shekarun da tayi cikin halin kunci da cin zarafi, Anastasia a tsorace take da mijinta don ta dinga tunanin me zata sanar dashi kafin ta barshi.

Bayan daukar bidiyon yadda ya zaneta, yayi barazana ga yayanta da mahaifinta a kan kada su sanar da jami'an tsaro.

Mai magana da yawun 'yan sandan yankin, Yulia Kuznetzova ta ce da farko an zargi magidancin ne da laifin cin zarafi amma ya koma laifin kisan kai ne bayan mutuwarta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng