MNJTF ta halaka babban alkalin ISWAP da wasu kwamandoji

MNJTF ta halaka babban alkalin ISWAP da wasu kwamandoji

- Rundunar sojin hadin guiwa ta kasa da kasa (MNJTF) ta halaka babban kwamanda mai matsayi na uku kuma alkalin ISWAP

- Hakan ya faru ne a harin da rundunar ta kai wa mayakan a ranar Asabar yayin da suka tattaru a wani sansanin horarwa

- An gano cewa, wasu manyan kwamandoji na Boko Haram din sun rasa rayukansu a wani hari na daban da aka kai musu a jiragen yaki

Rundunar sojin hadin guiwa ta kasa da kasa (MNJTF) ta halaka babban kwamanda mai matsayi na uku a ISWAP ko kuma Boko Haram mai suna Khalifa Umar.

Kamar yadda kakakin jami'an tsaron na hadin guiwa ya sanar, Colonel Timothy Antigha, ya ce an kashe Umar ne a ranar Asabar a Tunbum Sabon.

"An dade ana neman Khalifa Umar kasancewarsa babban alkalin ISWAP. A wani harin da aka kai musu ta jiragen yaki a Kwalaram, an halaka manyan kwamandojin ISWAP din har guda uku.

DUBA WANNAN: Ajali: Ladan ya mutu a cikin Masallaci yayin jiran lokacin kiran Sallar Asuba

"Za a sanar da sauran bayanai a kan yadda yakin ya kasance a zantawar da za'ayi da manema labarai nan gaba. Hakazalika, MNJTF ta hari wani sansanin horarwa na ISWAP dake yankin Tumbun Madayi a kwanaki uku da suka wuce kuma an samu sakamakon da ake bukata. Da yawa daga cikin 'yan ta'addan da kwamandojinsu sun sheka lahira bayan da suka tattaru don horarwa.

"Kamar yadda bayanin yakin ya nuna, an tarwatsa da yawa daga cikin kayayyakin more rayuwa na 'yan ta'addan. MNJTF din a shirye take wajen hada karfi da karfe da sauran jami'an tsaro na kasar nan don ayyukansu tare da matsawa ISWAP din har sai sun yada makamansu," takardar tace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel