Wata sabuwa: Shehu Sani ya kara fada wa 'tsaka mai wuya' a hannun hukumar EFCC
Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta daskarar da asusun bankin Shehu Sani, tsohon sanata mai wakiltar jihar Kaduna ta tsakiya, hadiminsa ya zargi hakan.
A wata takarda da babban mai bada shawara na musamman ga Sani, SuleimanAhmed, ya fitar a ranar lahadi, ya jajanta yadda aka tirsasa sanatan da ya bayyana kadarorinsa.
Hukumar EFCC din ta cafke Shehu Sani ne sakamakon zarginsa da ake da damfarar Sani Dauda wasu makuden kudade, a kan zai ba Ibrahim Magu don ya rinjayi wani bincike da hukumar ke yi.
Duk da tsohon dan majalisar ya musanta zargin, hukumar ta cigaba da bayyana cewa yana da tambayoyin da zai amsa a wajensu.
A wata takarda, hadimin Sani ya zargi EFCC da zama masu son kai kuma ya lissafo wasu tambayoyi da yake bukatar EFCC din ta ansa masa.
Ya yi mamakin yadda hukumar bata kama wanda ke zargin Sani ba duk da ya bayyana cewa ya bada cin hanci. Kuma wanne dalili ne yasa basu gayyaci Alhaji Samaila Isa Funtua ba wanda aka sako cikin zargin bata sunan Shehu Sani?
DUBA WANNAN: Dandalin sada zumunta: An yi 'caa' a kan Buhari bayan ganin takalmansa 'futu-futu' da kura yayin taro a Villa (Hotuna)
"Mene ne dangantakar damfarar makuden kudaden da kuma bincikar gidansa tare da daskarar da asusun bankunan tsohon sanatan?" ya tambayi EFCC.
Sauran tambayoyin sune kamar haka:
Me zaku ce a kan wanda yake zargin Shehu Sani wanda bai iya rubutu ba balle karatu, amma kuka sashi a hanyar da zai rubuta abinda ya faru?
Muna gano cewa, wanda ke zargin Sani bashi da wata shari'a a gaban kotun koli, me ya kai kudinsa hannun Shehu Sani don ya mika rashawa?
Babban alkalin kotun kolin ya musanta wannan zargin, haka Shehu Sani. A ina Orilade ya samo zargin rashawar?
Idan kuna da wata shaida ku bayyana ta da wuri. Wanda ke karar Shehu Sani yace $24,000 ku kuma kunce $25,000. A ina kuka samo karin $1,000?
Toni Orilade ya dena barazana ga mutane. Idan yana da wata sahida, ya fito ya bayyana.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng