Tsohon minista Maku ya karyata zargin kasancewa da hannu a shirin Atiku da Tinubu na kafa sabuwar jam’iyya

Tsohon minista Maku ya karyata zargin kasancewa da hannu a shirin Atiku da Tinubu na kafa sabuwar jam’iyya

Labaran Maku, wani tsohon ministan labarai a gwamnatin Goodluck Jonathan, ya karyata zargin kasancewa da hannu a cikin shirin da aka rahoto cewa tsohon mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar da babban dan siyasa, Bola Tinubu na yi, na kafa sabuwar jam’iyya gabannin 2023.

Maku ya kasance sakataren jam iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) na kasa, Atiku ya yi takarar shugaan kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) yayinda Tinubu ya kasance babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Hasashe sun nuna cewa Tinubu, tsohon gwamnan jihar Lagas na hararar kujerar Shugaban kasa gabannin 2023.

Maku wanda ya yi magana a ranar Lahadi, 12 ga watan Janairu, ya ce rahoton wanda ke ikirarin cewa ya gana tare da Atiku da Tinubu don kafa sabuwar jam’iyya na bogi ne.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Maku, wanda ya kasance dan takara na jam’iyyar APGA a zaben gwamnan 2019 a Nasarawa, ya yi magana ne a Wakama, karamar hukumar Akun da ke jihar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Allah ya yiwa Alkalin tarayya, Justis Ibrahim Maikaita Bako rasuwa

Tsohon ministan ya bukaci magoya bayansa da sauran yan Najeriya da su yi watsi da labarin domin wanzuwar zaman lafiya.

Maku ya alakanta rahoton zuwa ga wadanda ya zarga da sace masa kuri’unsa sannan ya kara da cewa suna tsoron magomarsa mai cike da haske.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel