Bayelsa: Dickson zai soma biyan sabon karin albashin da aka yi wa Ma’aikata
Gwamna Seriake Dickson na jihar Bayelsa ya amince a fara biyan ma’aikata sabon tsarin albashin ma’aikata na akalla N30, 000 a wata.
Seriake Dickson ya amince a fara biyan wannan albashi ne a karshen Watan Junairun nan da ake ciki kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.
Jaridar ta bayyana cewa Mai girma gwamnan ya bada wannan umarni ne a Ranar Juma’a 9 ga Watan Junairun 2020 a lokacin wani taro.
Gwamnan ya gana da shugabannin ‘Yan kwadago a Garin Yenagoa, inda ya umarci jami’an gwamnatinsa su soma biyan wannan kudi.
A jawabinsa, ya nuna godiyarsa ga kungiyoyin kwadago game da irin fahimtar da aka samu wajen wannan aiki a mawuyacin halin tattali.
KU KARANTA: Ban ce zan soma biyan sabon albashi ba - Gwamnan Filato
“Na yi maku alkawari cewa ba mu adawa da karin N30, 000 da gwamnatin tarayya ta yi. Yau na cika wannan alkawari na wa” Inji Dickson.
“Idan abubuwa su na tafiya daidai, babu abin da za mu biya hazikan ma’aikatanmu da za ace ya yi yawa. Ban san yadda zan gode maku ba.”
Gwamnan mai shirin barin gado ya kuma nuna cewa ya na sa rai kungiyar kwadago za ta yi aiki da kyau da gwamnatin da za ta karbi mulki.
A na su jawabin, shugabannin kungiyar NLC da TUC na jihar, John Ndiomu and da Layi Julius sun ji dadin wannan kari da aka yi wa ma’aikata.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng