Mamaki: Gwamnan Arewa da ya ci zabe a 2019 bashi da gidan kansa, motarsa daya ta hawa

Mamaki: Gwamnan Arewa da ya ci zabe a 2019 bashi da gidan kansa, motarsa daya ta hawa

Duk da kasancewar jiharsa ta gaba da 'yan ta'adda suke kaiwa hare-hare tare da aiyukan ta'addanci, Gwamna Babagana Umara Zulum mutum ne mai tsananin karfin hali da kwarin guiwa.

Jajircewarsa da kuma rashin bari 'yan ta'addan su zama babbar barazana gareshi, abin jinjina ne. Yana zuwa ko ina a cikin jihar kuma a duk lokacin da yaso. Hatta can cikin jihar borno inda ake kallo da tsananin hatsari ko yuwuwar kai hari, gwamnan na zuwa.

A cikin kwanakin nan ne gwamnan ke yawan kai ziyara asibitocin gwamnati a jihar, kuma a tsakar dare tun bayan da ya samu rahoton cewa likitoci na barin bakin aikinsu in dare yayi nisa. Wasu likitocin kan koma gida wanda hakan ke matukar tagayyara marasa lafiya.

DUBA WANNAN: Mayakan Boko Haram sun sace matafiya 7 a daf da Maiduguri

Gwamnan ya zage damtse wajen gina sabbin makarantu tunda sauran dake cikin jihar mayakan Boko Haram sun kone wasu kurmus.

Gwamnan, wanda aka gano dan babban malami ne, bashi da gidan kan shi kuma mota daya tak ya mallaka kafin ya zama gwamnan jihar Borno. Ya fito daga gidan dattako kuma da kanshi yayi fafutukar da har ya kai matsayin farfesa a fannin ilimi. Yayi aiki a matsayin direban mota tasi a wasu shekarun rayuwarsa.

Wanne gwamna aka sani wanda bashi da gidan kansa da kuma motar hawa daya tak? Wanne gwamna ne kuma yake kai ziyara assibitoci karfe daya na dare?

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel