Jaruman Kannywood sun raba wa almajirai kayayyaki a Kano

Jaruman Kannywood sun raba wa almajirai kayayyaki a Kano

Furodusa a masana'antar Kannywood, Hassan Giggs ya raba kayan sanyawa 1,000 ga almajirai a cikin birnin Kano. Tauraron yace halin da yaran ke ciki ya matukar taba shi ta yadda suke yawo a tituna. Yayi kira ga iyaye da su sauke nauyin yaransu yadda ya dace don gina al'umma ta gari.

"Mun lura cewa da yawan yaran na cikin wani hali ballantana a wannan sanyin da ya ta'azzara. Na lura cewa da yawan yaran basu da kayan sanyawa, wasu kuma basu da takalma. Toh ka gwada yadda rayuwa babu wadannan abubuwan zasu kasance," in ji shi.

Ya roki iyaye da su dau nauyinsu kuma su tabbatar da yaransu sun mallaki duk abinda suka dace kafin su turo yaran birni neman karatun addini.

DUBA WANNAN: Buhari ya bayar da umurnin gina gidaje 1,000 a jihar Borno

Hakazalika, wasu kungiyoyin taimakon kai da kai sun rabawa almajiran rigunan sanyi. Gidauniyar tallafi ta Today's Life dake Kano ta nemi tallafin kayan sanyawa da na abinci don raba wa almajirai.

Mai gidauniyar, Hajiya Mansura Isah tace "Na san wata tsangaya a Kano mai almajirai 5,000. Idan malamin zai ciyar da almajiran, buhuna 10 na shinkafa ba zai ishesu ba." Ta ce ta hanyar tallafi ne kawai za a iya samarwa yaran tallafi da abubuwan rayuwa na yau da kullum.

Ta bayyana tausayinta ga almajiran ta yadda ake wannan sanyin amma suna waje babu wani kayan arziki a jikinsu ballantana kayan sanyi.

"Duba yadda muke rufe daki tare da sanya kaya masu kauri da barguna amma kuma muna jin sanyin. Yaya kake tunanin yaran nan suke ji?" cewar Hajiya Mansurah Isah.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel