Iran ta bayyana cewa ita ta harbo jirgin Ukraine da yayi sanadiyyar mutuwar mutane 176

Iran ta bayyana cewa ita ta harbo jirgin Ukraine da yayi sanadiyyar mutuwar mutane 176

Kasar Iran ta amince da cewa ita ce ta harbo jirgin fasinjoji na kasar Ukraine wanda ya fadi a ranar Laraba yayi sanadiyyar mutuwar mutane masu yawan gaske

"Ranar bakin ciki, Muna juyayi da kuma mika ta'aziyya ga mutanen mu, da kuma iyalan duk wadanda abin ya shafa, da sauran al'ummomi na wasu kasashen," jawabin Ministan harkokin wajen Iran kenan Javad Zarif wanda yayi a yau Asabar.

Jirgin saman fasinjoji mai kirar Boeing 737-800 da kamfanin jiragen sama na kasar Ukraine ya mallaka ya fado kasa jim kadan bayan ya tashi daga filin tashi da saukar jiragen sama na birnin Tehran da misalin karfe 6:12 na safe. Duka fasinjoji 176 ciki kuwa hadda 'yan kasar Iran 82 sun mutu.

Tun farko dama an fara zargin cewa harbo jirgin aka yi domin kuwa lamarin ya faru ne a daidai lokacin da kasar ta Iran take harbawa kasar Amurka makamai masu linzami. a daren ranar Larabar. Amma kasar Iran din ta musanta hakan, inda wani babba a gwamnatin kasar yace ba kasar bace ta harbo jirgin.

Haka kuma ita ma kasar ta Ukraine tayi watsi da rahoton dake nuna cewa harbo jirgin aka yi, amma daga baya ta fara yadda bayan aka fara samo shaidar cewa harbo jirgin aka yi.

A ranar Alhamis dinnan da ta gabata, firaministan kasar Canada, Justin Trudeau ya bayyana shaidar cewa kasar Iran ce ta harbo jirgin. Kasar Canada dai tana da mutane mafi yawa da suka mutu a cikin jirgin banda kasar Iran, domin kuwa tana da mutane 63, haka kasar Jamus da Birtaniya da Ukraine duka suna da mutane a cikin jirgin.

Kasar ta Iran ta ce za ta nemi goyon baya daga abokan huldar kasar musamman kasar Faransa da Canada, don nazarin shaidar da aka tattara game da hadarin jirgin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel