Hamshakin mai kudi a kasar Japan ya rabawa mabiyanshi na Twitter Dala Miliyan 9

Hamshakin mai kudi a kasar Japan ya rabawa mabiyanshi na Twitter Dala Miliyan 9

- Wani biloniya a kasar Japan, Yusaku Maezawa ya fito da wata gasa inda zai ba mutane 1,000 a tuwita makuden kudi

- Yace zai bada kudin ne don ganin yadda mutane 1,000 din zasu shiga farin ciki da habakar rayuwa

- Ko a watan Janairu na 2019, Maezawa ya yi wannan gasar inda ya ba mutane 100 kyautar makuden kudade

Babban mashahurin mai kudi a kasar Japan, Yusaku Maezawa ya sanar da cewa zai bada kyautar $9 million ga mutane 1,000 a tuwita don ganin yadda farin cikin mutanen zai habaka.

Babban mai kudin ya sanar da hakan ne a wata sanarwa da yayi a wani bidiyo a YouTube. Ya sanar da cewa zai gwada ya ga yadda hakan zai taba rayukan mutane 1,000 ne.

Biloniya din ya samu goyon bayan dan takarar shugabancin kasa Andrew Yang, kuma an hori masu bukatar tallafin da su sake wallafa rubutun da yayi a ranar 1 ga watan Janairu kafin su bada dalilin da yasa suke bukatar kudin.

Kusan kowa zai iya shiga gasar wanda aka rufe a ranar 7 ga watan Janairu. Sama da mutane miliyan 4 ne suka fito gasar kuma za a buga caca ne kafin a gano wadanda za a zaba.

KU KARANTA: Tirkashi: Wani mutumi ya siyawa karuwarshi dankareren gida, bayan matarshi ta neme ta da fada

Maezawa da kan shi zai sanar da masu nasara ta hanyar tura musu sakon kar ta kwana a cikin kwanaki uku kuma za a ga yadda kudin ya bada gudummawa a rayuwarsu.

Ya yi irin wannan gasar a 2019 kuma yayi alkawarin Yen miliyan 100 ga masu amfani da tuwita100.

Biloniyan kasar Japan din ne fasinja na farko da ya hau jirgin kanshi don zagaye wata tare da Elon Musk. An gano kuma yana kashe kudi masu tarin yawa a kere-kere, motoci na alfarma da sauran abubuwan more rayuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel