Kwamacala: Wata mata ta haifi tagwaye wanda kowanne ubansa daban

Kwamacala: Wata mata ta haifi tagwaye wanda kowanne ubansa daban

- Asirin wata mata a kasar China da aka boye sunanta ya tonu a kan cin amanar mijinta da take yi bayan ta haifa 'yan biyu masu banbanci mai yawa

- Mijin mai suna Xiaolong ya mika tagwayen asibiti inda aka gano iyayensu maza daban ne ta hanyar gwajin kwayar halittar DNA

- Bayan musantawa da mahaifiyar tayi, daga baya ta bayyana cewa tayi lalata na tsawon dare daya da wani mutum wanda ba mijinta ba

Wata mata ta rasa yadda zata yi da ya wuce ta bayyana gaskiya a kan cin amanar mijinta da tayi bayan gwajin kwayar halitta ya bayyana cewa 'yan biyun da ta haifa ba na mijinta bane shi kadai.

Matar 'yar asalin kasar China ta haifa yara maza tagwaye ne amma sam basu kama da juna, lamarin da ya kawo tashin-tashina kuma yasa mijin yace a yi gwajin kwayar halitta na DNA.

Daraktan Fujian Zhengtai Forensic Identification Centre ya sanar da Xiaolong cewa daya daga cikin tagwayen ne nashi. A nan ne mahifiyar ta bayyana gaskiyar lamarin. Akwai wani dare daya da ta share tana lalata da wani mutum da ba mijinta ba.

KU KARANTA: Iyaye sun kashe 'yarsu da duka saboda tana soyayya da saurayi Bayerabe

Kamar yadda kwararru suka bayyana, ana iya samun wannan lamarin amma da matukar wahala.

Xiaolong ya ce dan shi kadai zai karba amma ba dan wani kato ba da ya kwanta da matar shi. Mutane da yawa sun ga kokarin shi don idan wani ne, saki ne zai biyo baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel