Iyaye sun kashe 'yarsu da duka saboda tana soyayya da saurayi Bayerabe

Iyaye sun kashe 'yarsu da duka saboda tana soyayya da saurayi Bayerabe

- Matashiyar budurwa mai suna Amaka ta hadu da ajalinta ne bayan iyayenta sunyi mata mugun duka a kan soyayya da Bayerabe

- Kiyayyarsu ga Ibrahim ta fara bayyana ne tuntuni amma bata yi kamari ba har sai da Amaka ta samu ciki kuma ya amince nashi ne

- Bayan kwanaki da haihuwarta ne taje ta karbo kaya da kudi na bukukuwan sabuwar shekara, lamarin da yasa iyayenta yi mata mugun dukan da yayi ajalinta

Matashiyar budurwa mai suna Amaka ta hadu da ajalinta a hannun iyayenta. Amaka ta fara soyayya ne da saurayinta mai suna Ibrahim Lawal tun tana babbar makarantar sakandire a garin Legas. Soyayyarsu tayi nisa don iyayen Ibrahim tuni suka amince da lamarin. Ba nan gizo ke saka ba, iyayen Amaka kwata-kwata basu son ganinta da Ibrahim don an sha yi mata mugun duka a kan tarayya da Bayerabe. Iyayen nata 'yan asalin yankin Kudu maso gabas ne na kasar nan.

Babban tashin hankalin ya fara ne bayan da Amaka ta samu ciki kuma Ibrahim da iyayenshi suka tabbatar da nasu ne. Su kan kai mata kayan abinci da kudi tare da zuwa ganin lafiyarta lokaci zuwa lokaci.

A bangaren iyayen Amaka kuwa, duka kala-kala ta sha shi, hakazalika su kan azabtar da ita da yunwa duk da juna biyun dake jikinta. Sun kuma hana ta ganin Ibrahim kwata-kwata.

KU KARANTA: Mijina na turawa karuwarshi hotuna na tsirara domin ya muzantani a wajen ta - Matar aure ta koka

Wata makwabciyarsu mai suna Ebunola ta bayyana cewa "muna ganin azabtarwa da ake wa yarinyar duk da tana dauke da ciki. A lokacin da aka kaita asibiti har ta haihu, sun rasa kudin biya. Sai suka kira 'yan uwan Ibraheem kuma babu bata lokaci suka biya kudin. A ranar suna kuwa, sai da dattijan yankin suka saka baki sannan suka bada jaririn ga iyayen Ibrahim."

Mahaifiyar Ibrahim ta ce "rigimar ta fara ne bayan da Amaka tazo ta karba kayan bikin sabuwar shekara a hannuna. Mun bata kayanta da na jaririn tare da kudi. Bayan isarta gida ne suka kulleta a daki na kwana biyu suna dukanta. Ta kwanta rai a hannun Allah sannan suka kaita asibiti. Munje mun ganta amma jikin babu dadi. A nan ne ta ce ga garinku."

Mike Nweke, mahaifin Amaka ya musanta cewar su suka kashe diyarsu da kansu, lamarin da makwabta da duk wanda ya san su ya musanta.

A lokacin da aka tuntubi Ibrahim, ya kasa cewa komai baya ga kukan da yake yi.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Legas, DSP Bala Elkana, ya ce suna jiran rahoton dalilin mutuwarta kafin su dau mataki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel