Gwamna Zulum ya kwana tare da yan gudun hijira, ya raba barguna 1,675

Gwamna Zulum ya kwana tare da yan gudun hijira, ya raba barguna 1,675

Gwamnan jahar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya kwana a wani sansanin yan gudun hijira inda ya raba ma yan gudun hijiran bargunan rufa guda 1,675 domin maganin sanyi.

Daily Trust ta ruwaito gwamnan ya kai ziyarar ba zata ne zuwa sansanin na NYSC da misalin karfe 10:15 na daren Alhamis inda ya raba ma masu sansanin yan gudun hijira su 1675 barguna. Inda yace ya kai ziyarar ne domin ganawa da jama’an domin jin matsalolin da suke fuskanta.

KU KARANTA: Badakalar $24000: Ba zan taba yin shiru wasu na fadin karairayi a kai na ba – Shehu Sani

Gwamnan ya raba ma mazauna sansanin barguna, tabarma da sauran kayan sawa, tare da tabbatar musu da manufarsa na mayar da su gidajensu, sa’annan yace zai basu dukkanin gudunmuwar da suke bukata don cigaba da rayuwarsu.

Haka zalika Gwamna Zulum ya ba su tabbacin gwamnatin tarayya na kawo karshen yaki da Boko haram, sa’annan ya yi kira ga jama’a da su bayar da dukkanin bayanan da za su taimaka ma jami’an tsaro wajen kawo karshen ta’addanci.

A wani labarin kuma, gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta biya tsofaffin ma’aikatan tsohuwar hukumar sadarwa ta Najeriya NITEL da MTEL da yawansu ya kai mutum 11,331 hakkokinsu na fansho da ya kai naira miliyan 842.8.

Shugabar hukumar tsarin biyan fansho na wucin gadi, PTAD, Chioma Ejikeme ce ta bayyana haka, inda tace sun biya wadannan kudade ne a watan Disambar da ta gabata.

Uwargida Chioma ta bayyana cewa biyan kudin na daga cikin tsarin gwamnatin tarayya na rage yawan hakkokin yan fansho da tsofaffin ma’aikata dake wuyanta, sa’annan ta tabbatar ma yan fansho cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mayar da hankali wajen tabbatar da walwalarsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel