Gwamnati ta gargadi gidajen abinci dake amfani da maganin Paracetamol wajen sarrafa gari

Gwamnati ta gargadi gidajen abinci dake amfani da maganin Paracetamol wajen sarrafa gari

- Gwamnatin jihar Osun tayi kira da kakkausar murya ga masu gidajen siyar da abinci da kuma masu sarrafa rogo zuwa gari

- Fannin duba gari na cibiyoyin kiwon lafiya na jihar sun bankado yadda ake amfani da fanado da kuma hypo wajen girki

- Gwamnatin jihar ta bayyana illolin hakan tare da matsalolin da suke haifarwa

Gwamnatin jihar Osun tayi kira ga masu abincin siyarwa a jihar da su bar mummunan salon da suke amfani dashi wajen dafa nama da sarrafa rogo zuwa gari.

Sau da yawa masu gidan cin abinci kan yi amfani da kwayar fanadol don tausasa nama yayin dahuwa kuma suna amfani da hypo a wajen sarrafa rogo zuwa gari don yayi fari tas.

Wannan jan kunnen anyi shi ne a taron manema labarai da mai bada shawara ta musamman a kan lafiya, Pharm. Siji Olamiju da kwamishinan yada labarai da wayar da kai, Funke Egbemode suka yi a kan illar hakan ga muhimman sassa na jiki.

Olamiju ta bayyana cewa hakan na zama barazana ga lafiyar jama'a wanda duba gari na fannin kiwon lafiya a jihar suka bankado.

A yayin kwatanta lamarin da ta'addanci tare da mugun rashin sani, Olamiju tayi kira ga masu aikata wannan mugun aikin da su dena saboda tsananin illar hakan ga lafiyar masu amfani da abincin a jihar.

KU KARANTA: Duk wanda ya iya warkar dani nayi alkawarin siya mishi gida a Turai - Gurgu ya kalubalanci Fastoci

Mai bada shawarar ta bayyana cewa, hypo ana amfani da shi ne wajen sanya kaya suyi haske amma ba a so koda fata ya taba balle cikin dan Adam.

Egbemode ta bayyana cewa jihar ta yanke shawarar wayar da kan jama'a a kan illolin gubar tare da ilimantar da masu siyar da abinci da masu sarrafa rogo zuwa gari.

Ta kara bayyana cewa fanado ana amfani dashi ne don kashe ciwo amma sai a saka shi wajen dafa nama da ganda don rage kudin itace ko kalanzir da kuma lokacin girkin.

Ta kara da jajanta yadda ake amfani da hypo don sarrafa rogo zuwa gari. Hypo din na lalata kayan ciki ta yadda zai kashe mutum a hankali.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel