Sunaye: BUK ta daga darajar lakcarori 15 zuwa Farfesa

Sunaye: BUK ta daga darajar lakcarori 15 zuwa Farfesa

Majalisar zartarwa ta jami’ar Bayero dake Kano ta amince da karin girman wasu manyan malamai zuwa farfesoshi, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Wanna takardar ta samu saka hannun daraktar jarabawa, guraben karatu da adana ne ta jami’ar, Amina Abdullahi, wacce ta ce an yanke wannan hukuncin ne a taron majalisar karo na 379 wanda aka yi a ranar Laraba, 24 ga watan Disamba, 2019.

Kamar yadda takardar ta bayyana, sun samu karin girman ne tun daga ranar 1 ga watan Oktoba na 2019.

“Majalisar zartarwar ta amince da karin girman wadannan malaman nata”, cewar takardar.

DUBA WANNAN: Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana makomar El-Zakzaky

“Wadanda suka samu karin girman sun hada da daraktan cibiyar karantar da Qur’ani, Farfesa Muhammad Babangida Muhammad a matsayin farfesa, Farfesa Nuratu Mohammed da Haruna Musa a yanzu duk farfesoshi ne.” in ji takardar.

“Sauran sun hada da Dr. Salihu Said, Dr. Hassana Sani Darma, Dr. babatunde Olamide Bamgbose, Dr. Amina Abubakar Ismail, Dr. Shehu Usman Yahaya da Dr. Ahmed Maigari Ibrahim duk a halin yanzu farfesoshi ne,” cewar takaradar.

Har ila yau, takardar na kunshe ne da sunayen manyan lakcarori 28 da aka kara wa girma, sun hada da, Dr. Musa A.Auyo, Dr. Hajara Umar Sanda, Dr. Nu’uman Muhammad Habib, Dr. Bala Saleh Dawakin Tofa, Dr. Garba Iliyasu, Dr. Ibrahim Mu’azzam Saminu Maibushira, Attah Raphael Avidire da Dr. Omoje Uchenna Kelvin da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel