Buhari ya biya tsofaffin ma’aikatan NITEL/MTEL su 11,331 hakkokinsu na fansho N842.8m
Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta biya tsofaffin ma’aikatan tsohuwar hukumar sadarwa ta Najeriya NITEL da MTEL da yawansu ya kai mutum 11,331 hakkokinsu na fansho da ya kai naira miliyan 842.8.
Shugabar hukumar tsarin biyan fansho na wucin gadi, PTAD, Chioma Ejikeme ce ta bayyana haka, inda tace sun biya wadannan kudade ne a watan Disambar da ta gabata, kamar yadda rahoton jaridar Daily Trust ta bayyana.
KU KARANTA: Mai dokar barci: An kama masu gadin bututun mai su 20 da laifin satar man fetir
Uwargida Chioma ta bayyana cewa biyan kudin na daga cikin tsarin gwamnatin tarayya na rage yawan hakkokin yan fansho da tsofaffin ma’aikata dake wuyanta, sa’annan ta tabbatar ma yan fansho cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mayar da hankali wajen tabbatar da walwalarsu.
Ta kara da cewa tun a watan Feburairun 2018 suka fara aikin tantance yan fanshon NITEL da MTEL domin tabbatar da sahihancinsu, tare da sanya su cikin tsarin biyan fansho na wata wata kamar yadda dokar gyaran fansho na shekarar 2014 ta bata dama.
“Wannan shi ne abin da mika yi ga tsofaffin ma’aikatan kamfanin karafa na Delta, Nigeria Reinsurance, hukumar gidaje ta gwamnatin tarayya, NICON da kuma fararen hula na kwalejin horas da hafsan Sojin Najeriya.
“Duk wani dan fansho ya cancanci a ba shi kulawar da ta dace duba da shekarun da ya yi wajen bauta ma kasa, wannan yasa ma’aikatan PTAD da shuwagabanninta za su cigaba da aiki tukuru don tabbatar da yan fansho suna samun kudinsu a lokacin daya kamata.” Inji ta.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng