Boko Haram ta kashe hazikan sojoji 3 da yan farar hula 8 a Monguno

Boko Haram ta kashe hazikan sojoji 3 da yan farar hula 8 a Monguno

Rahotanni sun kawo cewa yan ta’addan Boko Haram sun kashe wasu sojiji uku sannan suka jikkata wasu takwas a Monguno, jihar Borno a ranar Talata.

An tattaro cewa motar yan ta’addan cike da abubuwan fashewa sun shigi ayarin motocin sojojin.

Hakan ya faru ne kasa da kwanaki 10 bayan janye dakarun kasar Chadi da ke taya takwarorinsu na Najeriya wajen yaki da yan ta’addan ISWAP a iyakar tafkin Chadi a arewacin jihar Borno.

Wata majiya ta soji ta ce dakarun sun yi arangama da yan ta’addan a shataletalen Monguno.

An tattaro cewa yan ta’addan sun kuma kona laima sama da 300 sannan sun kashe mutane takwas da jikkata wasu a sansanin yan gudun hijira a Monguno, kilomita 100 daga Maiduguri.

Yan ta’addan sun mayar da mutane sama da 1000 marasa galihu sannan suka tsere da magunguna a wurare daban-daban.

KU KARANTA KUMA: Shugaban kwamitin karbar mulki ya yanke jiki ya fadi mattace bayan kammala taro a Abia

A wani labarin kuma, mun ji cewa Mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram sun kira ma kansu ruwa yayin da suka yi gangami suka kai samame zuwa sansanin rundunar Sojin kasar Nijar, amma sai reshe ya juye da mujiya, inda Sojojin Nijar suka karkashe su, kisan kiyashi.

Rahoton gidan talabijin na Channels ta bayyana cewa a yayin wannan musayar wuta da aka yi a ranar Alhamis, Sojojin Nijar sun halaka mayakan Boko Haram har guda 63. Kaakakin Sojin Nijar, Kanal Souleymane Gazobi ya tabbatar da lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel