Boko Haram ta dandana kudarta a hannun Sojojin Nijar, sun kashe 63

Boko Haram ta dandana kudarta a hannun Sojojin Nijar, sun kashe 63

Mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram sun kira ma kansu ruwa yayin da suka yi gangami suka kai samame zuwa sansanin rundunar Sojin kasar Nijar, amma sai reshe ya juye da mujiya, inda Sojojin Nijar suka karkashe su, kisan kiyashi.

Rahoton gidan talabijin na Channels ta bayyana cewa a yayin wannan musayar wuta da aka yi a ranar Alhamis, Sojojin Nijar sun halaka mayakan Boko Haram har guda 63. Kaakakin Sojin Nijar, Kanal Souleymane Gazobi ya tabbatar da lamarin.

KU KARANTA: Malaman jami’a sun ki cewa uffan bayan sun goga gemu da gemu da Buhari a Villa

Gazobi ya ce: “Da misalin karfe 1 na rana yan ta’addan Boko Haram a kan babura da motoci suka kai hari Chinegodar a yammacin Tillaberi, nan da nan dakarun Sojan kasa da na sama suka amsa tare da taimakaon abokan aikinmu yan kasan waje.

“Inda muka yi ta luguden wuta a kansu har sai da muka rakasu wajen iyakarmu, sai dai Sojojinmu guda 25 sun mutu, yayin da yan ta’adda 63 suka mutu a banza.” Inji shi.

Wannan hari ya faru ne a daidai wajen da yan Boko Haram suka kashe Sojojin Nijar 71 a wani hari da daruruwan yan ta’adda suka kai musu a a sansaninsu a watan Disambar shekarar 2019, wannan hari shi ne mafi muni da yan ta’adda suka kai ma Sojin Nijar.

A wani labari kuma, Gungun mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram dauke da muggan makamai sun tare wasu motocin sufuri guda biyu a jahar Borno, inda suka kwashe fasinjoji 7, suka yi awon gaba da su.

Wani fasinja da ya sha da kyar kuma ya nemi a sakaya sunan sa ya bayyana cewa yan ta’adda a cikin motocin Hilux guda 2 sun tare motoci guda biyu da suka hada da Golf da Hiace na kamfanin Adamawa Sunshine.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel