An samu gawar tsohon dan majalisa da hadimansa biyu a cikin mota

An samu gawar tsohon dan majalisa da hadimansa biyu a cikin mota

- Jami'an 'yan sanda a ranar Alhamis a kasar Phillippine sun tsinci gawar wani tsohon dan majalisa tare da hadimansa biyu

- An ga gawar tsohon dan majalisar, Edgar Mendoza ne a kan gadar birnin Tiaong dake yankin Quezon

- Jami'an 'yan sandan sun ga wasu kayan mamatan a tazara kadan daga inda aka samu gawawwakin

Jami'an 'yan sanda a ranar Alhamis a kasar Philippine sun tsinci gawar wani tsohon dan majalisa tare da mai tsaron lafiyarsa da kuma direbansa a kone cikin motarsa.

An ga gawar tsohon dan majalisar Edgar Mendoza ne tare da hadimansa biyu a mazaunin baya na motarsa a kan gadar birnin Tiaong dake yankin Quezon, birni dake kilomita 85 daga kudancin Manila.

DUBA WANNAN: Tsugune bata kare ba: An fara yi wa 'yan Najeriya mazauna Afirka ta kudu sabuwar barazana

"Yan sandan sun samu kira ne sakamakon wutar dake ci a motar tun kafin ketowar alfijir," Manjo Lawrence Panganiban, shugaban 'yan sandan Tiaong ya ce.

An tabbatar da cewa motar mallakin Mendoza ce, dan majalisar wakilai daga shekarar 1998 zuwa 2001, kuma shugaban hukumar shige da fice a kasar a da.

"Ya kasance lauya mai zaman kansa tun bayan da ya bar majalisar.

"Ya bar gidansa ne a ranar Laraba don haduwa da wani a yankin Laguna," Paniganiban ya ce.

Ya kara da cewa, 'yan sandan zasu yi binciken kwayar halitta a kan gawawwakin mamatan.

"Wasu daga cikin abubuwan mamatan an samesu a mitoci kadan daga konanniyar motar. Zamu yi duk abinda ya dace don ganin mun shawo kan matsalar," Paniganiban ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel