Hukumar Hizbah ta kashe auren dole 330 da akayi a jihar Jigawa

Hukumar Hizbah ta kashe auren dole 330 da akayi a jihar Jigawa

Hukumar Hizbah, shiyar jihar Jigawa a ranar Alhamis ta sanar da cewa ta kashe auren dole 330 da aka gudanar a shekarar 2019 bayan amaren sun gudu daga gidajen.

Shugaban hukumar, Ibrahim Garki, ya bayyanawa Premium Times cewa sun kashe auren dolen ne bayan amaren suka kai kara ofishohin Hizbah dake jihar.

Ya ce bayan kashe auren, hukumar ta mayar da amaren wajen iyayensu.

Hakazalika hukumar ta baiwa iyayen shawara su sanya 'yan matan makaranta.

Ibrahim Garki ya kara da cewa yawancin yan matan da aka yiwa auren dolen kananan yara ne da kuma zaurawan da iyayensu suka tilastasu auren mazaje ba tare yardarsu ba.

Bugu da kari, ya ce hukumar Hizban ta samu nasarar dakile wasu auren dolen da aka shirya.

DUBA NAN: Yan bindiga sun kai hari makaranta a Kaduna, sun sace dalibai 4

A wani labarin daban, hukumar Hizbah ta sanar da kama wasu matasa 15 da suka bayyana cewa 'yan 'luwadi' ne a jihar Kano.

Da yake tabbatar da kama matasan, mataimakin kwamandan Hisbah mai kula da aiyuka na musamman, Muhammad Al-Bakary, ya ce matasan da suka kama suna shirya biki na matasa masu sha'awar jinsi ne.

Ya kara da cewa dakarun hukumar Hisbah sun kai samame gidan da matasan da suka shirya bikin murnar kammala karatun Jami'a a wani gida dake unguwar Sabuwar Gandu a Kano.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel