APC: Tinubu ya yi magana a kan gadon kujerar shugaban kasa a 2023

APC: Tinubu ya yi magana a kan gadon kujerar shugaban kasa a 2023

Jagoran jam'iyyar APC a kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya ce babu bukatar tun yanzu a fara cece-kuce a kan batun waye zai gaji kujerar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a shekarar 2023. A cewarsa, masu maganar gadon kujerar shugaban kasa yanzu basa kishin Najeriya.

Kazalika, ya kare shugaba Buhari a kan zargin cewa yana kitsa yadda zai sake zarce wa a kan mulki a karo na uku.

Tinubu ya bayyana hakan ne ranar Talata bayan wata ganawarsa da shugaba Buhari a fadarsa, Aso Villa, dake Abuja.

Tsohon gwamnan na jihar Legas ya ziyarci shugaba Buhari ne domin yi masa murnar shigowar sabuwar shekara da kuma tattauna wasu batutuwa da suka shafi kasa.

"Ba maganar yanzu bace. Kwanan nan muka kammala wani zaben kuma har yanzu shugaban kasa yana aiki ne wajen saita al'amuran kasar nan," a cewar Tinubu yayin amsa tambayar manema labarai a kan waye zai gaji shugaban kasa da kuma yankin da zai fito.

APC: Tinubu ya yi magana a kan gadon kujerar shugaban kasa a 2023
Tinubu da Buhari
Asali: UGC

Sannan ya cigaba da cewa, "duk da ba za a hana jama'a tattauna wa a kan harkokin siyasa ba, babu wani mai kishin Najeriya da zai fara magana a kan shirin gadar kujerar shugaban kasa a 2023. Wannan iya ce maganar gaskiya. Kamata ya yi mu mayar da hankali wajen ganin kasa ta cigaba da samun yalwar arziki, yadda zamu taimaka wa shugaban kasa ya taimaki Najeriya. Babu abin da yafi yin hakan dace wa a halin yanzu."

DUBA WANNAN: Biyu babu: APC ba zata shiga zaben mayen gurbi ba a jihar Neja - INEC

Kazalika, Tinubu ya gaggauta yin watsi da zargin cewa shugaba Buhari yana kulla yadda zai sake zarce wa a kan kujerarsa a karo na uku.

"Buhari mutum ne mai kima da daraja da ba zai fara ma irin wannan tunanin ba koda wasu sun yi kokarin cusa masa ra'ayin hakan. Nayi imani da Buhari, na yarda da shi kuma ya kamata dukkan 'yan Najeriya su aminta da shi.

"Shugaban kasa da kansa ya sanar da 'yan Najeriya cewa zai sauka daga mulki a shekarar 2023, a cikin sakonsa na sabuwar shekara," a cewarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel