Malaman jami’a sun ki cewa uffan bayan sun goga gemu da gemu da Buhari a Villa

Malaman jami’a sun ki cewa uffan bayan sun goga gemu da gemu da Buhari a Villa

Shuwagabannin kungiyar Malaman jami’o’in Najeriya, ASUU sun ki yarda su bayyana ma manema labaru sakamakon tattaunawar da suka yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar gwamnati Aso Rock Villa game da IPPIS.

A ranar Alhamis, 9 ga watan Janairu ne ASUU ta yi ma Villa tsinke inda ta nemi ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari domin tattaunawa a kan tirka tirkan dake dabaibaye da tsarin biyan albashi na bai daya, IPPIS wanda Buhari ya umarci duk ma’aikatun gwamnatin tarayya su shiga.

KU KARANTA: Tsuguni bata kare ba: Miyagun yan bindiga sun halaka mutane 12 a jahar Filato

Malaman jami’a sun ki cewa uffan bayan sun goga gemu da gemu da Buhari a Villa
ASUU Buhari
Asali: Facebook

ASUU, a karkashin jagorancin shugabanta, Farfesa Abiodun Oguyemi ta yi fatali da wannan umarni na shugaban kasa, saboda a cewarsu tsarin zai gurgunta ayyukan malamai a jami’o’in Najeriya tare da kawo tsaiko ga tsarin koya da koyarwa.

Shi dai wannan tsari na IPPIS gwamnati ta kirkiro shi ne da nufin rage rashawa, satar dukiyar jama’a, saukaka samun da biyan albashi da kuma toshe duk wasu ramuka da kudaden gwamnati ke sulalewa.

Malaman jami’a sun ki cewa uffan bayan sun goga gemu da gemu da Buhari a Villa
ASUU Buhari
Asali: Facebook

Sai dai a lokacin da malaman wasu jami’o’i suka amsa kiran gwamnati wajen shiga tsarin, wasu malaman kuma basu yarda an gudanar da aikin a makarantunsu ba saboda matsayin hawa dokin na ki da ASUU ta yi.

Daga cikin wadanda suka halarci zaman akwai shugaba Buhari, ministan kudi, Zainab Shamsuna Ahmad, ministan watsa labaru, Lai Mohammed, ministan kwadago, Chris Ngige da ministan ilimi, Adamu Adamu, kamar yadda kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito.

Gwamnati ta dauki alwashin dakatar da albashin duk ma’aikacin da bai shiga IPPIS ba, yayin da ASUU ta dauki alwashin shiga yajin aiki na gama gari idan har gwamnati ta dakatar da albashin wani Malami saboda IPPIS.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel