Hamid Ali ya tara ma gwamnatin Buhari naira tiriliyan 1.3 a hukumar kwastam

Hamid Ali ya tara ma gwamnatin Buhari naira tiriliyan 1.3 a hukumar kwastam

Hukumar yaki da fasa kauri ta sanar da samun gagarumar nasara a shekarar 2019 inda ta tara makudan kudi da suka kai naira tiriliyan 1.341 a matsayin kudaden shiga daga harajin da take amsa daga watan Janairu zuwa Disamba na shekarar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito kwastam ta sanar da haka ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Joseph Attah ya fitar a ranar Alhamis, inda ta ce kudin da ta tara ya haura hasashenta da kimanin naira biliyan 404.

KU KARANTA: Tsuguni bata kare ba: Miyagun yan bindiga sun halaka mutane 12 a jahar Filato

A farkon shekarar 2019, hukumar ta yi has ashen tara naira biliyan 937, amma sai ga shi ta tara kudaden da suka fi haka yawa. Wadannan kudade sun fi na shekarar 2018 da hukumar ta tara na naira biliyan 139, inda a wancan lokaci ta tara naira tiriliyan 1.202.

Da yake tsokaci a kan nasarar, shugaban hukumar kwastam, Hamid Ali, ya danganta nasarar da suka samu ga dagewa a kan yin abin da ya kamata wajen bin doka da ka’ida, a maimakon biye ma son ran wasu mutane na biya ma kansu bukata fiye da duba amfanin da kasa za ta samu.

Ali yace kudaden da suke samu suna karuwa ne sakamakon sauye sauyen da suka samarwa a hukumar, daga cikin akwai tura jami’an da suka kamata don gudanar da ayyuka, dabbaka dokokin haraji.

Sauran sun hada da mayar da yawancin ayyukan hukumar zuwa na’ura mai kwakwalwa, wayar da kawunan masu ruwa da tsaki da kuma kiraye kiraye ga jami’an hukumar su sanya kishin kasa fiye da bukatar kansu.

Haka zalika Ali ya kara da cewa rufe iyakokin Najeriya da aka sun tilasta ma sundukan da ya kamata a yi fasa kaurinsu ta iyakoki, komawa bi ta cikin ruwa, wanda hakan ya kara adadin kudaden da ake samu a tashoshin ruwan Najeriya.

“Kafin kulle boda a ranar 20 ga watan Agusta, muna tara kimanin naira biliyan 4 zuwa biliyan 5 a kowanne rana, amma daga kulle boda zuwa yanzu muna samun naira biliyan 5 zuwa biliyan 7 a kullum.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng