Saudiyya ta yi 'tir' da kasar Iran a kan kai wa Amurka hari

Saudiyya ta yi 'tir' da kasar Iran a kan kai wa Amurka hari

Kasar Saudi Arabia ta yi 'tir' da harin daukan fansa da kasar Iran ta kai wa sansanin sojojin kasar Amurka dake kasar Iraqi tare da bayyana hakan a matsayin rashin girmama kasar Iraqi a matsayinta na kasa mai cin gashin kanta.

"Daular Saudi Arabia ta yi 'Allah - Wadai' da keta haddin kasar Iraqi da Iran ta yi," kamar yadda kasar ta bayyana a cewar shafin kamfanin dillancin labarai na SPA.

An dade ba a jituwa a tsakanin kasar Saudiyya mai biyayya ga mazhabar 'Sunni' da kuma kasar Iran mai biyayya ga mazhabar 'Shi'a'.

A ranar Laraba ne Iran ta kaddamar da wasu hare - hare da makamai masu linzami a wasu sansani guda biyu na sojojin kasar Amurka dake kasar Iraqi.

Hare - haren da kasar Iran ta kai wa sansanin sojin kasar Amurka na zuwa ne bayan wasu sa'o'i da binne gawar janar Soleimani.

A makon jiya ne kasar Amurka ta kashe babban hafsan rundunar sojojin kasar Iran, Janar Qassem Soleimani, a wani hari da ta kai masa a kasar Iraq ta hanyar amfani da wani jirgin yaki mai layar zana da ake sarrafa shi daga nesa ta na'ura mai kwakwalwa.

A ranar Laraba ne babban sakataren majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres, ya sanar da cewa zai cigaba da tattauna wa da kasashen biyu domin ganin an samu lafawar amon gangunan yaki da kowanne bangare ke buga wa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng