Jerin abubuwa guda 5 na Kannywood da za su dauki hankulan mutane a shekarar 2020

Jerin abubuwa guda 5 na Kannywood da za su dauki hankulan mutane a shekarar 2020

- Sanannen abu ne idan aka ce Kannywood na samar da aiyuka ga matasa a Arewacin Najeriya

- Sai dai akwai matsaloli masu tarin yawa da masana'antar take fuskanta

- A wannan shekarar, akwai abubuwa masu yawa da masana'antar ke son cimma wa

Sanannen abu ne idan aka ce masana'antar Kannywood waje ne mai dumbin mutane da ke aiki, musamman a Arewacin Najeriya.

A shekaru kadan da suka wuce, masana'antar ta shiga matsanancin hali, inda har wasu ke zargin zata durkushe, musamman kasancewar kasuwancin masana'antar ya tabarbare. Hakan kuma ya sa wasu mashirya fina-finan labewa inda suka yi shiru. Da dama daga cikin su suna da shirye-shirye masu kyau amma gudun asara yasa suka adana.

A don haka ne Aminiya ta rairayo abubuwan da zasu dauki hankali a masana'antar a wannan shekarar ta 2020.

1. Nafisa Abdullahi za ta zama darakta

Jaruma Nafisa Abdullahi ta wallafa a shafinta na Instagram a watannin baya cewa za ta zama darakta a karon farko. Tace zata zama darakta a karon farko a fim dinta mai suna Zainab Ali.

2. Bashir Maishadda da Jammaje zasu shirya fim 'mafi girma' a Kannywood

Furodusan da ba ya tsoron kashe kudi wajen shirya fim a Kannywood shi ne Abubakar Bashir Maishadda. Ya kuwa bayyana cewa shi da furodusa Kabiru Jammaje zasu shirya fim mafi girma a Kannywood. Za a fara daukar fim din ne a wannan watan na Janairu.

KU KARANTA: Tashin hankali: Lauya ta fadi ta a daidai lokacin da ta tona asirin makauniyar bogi

3. Adam A. Zango a Legas

Wani abin da masu kallo zasu sanya ido su gani shine kasancewar jarumi Adam Zango a jihar Legas.

A kwanakin baya ne ya bayyana a wata hira cewa zai koma kudu da harkokinshi. Ya ce zai fi mayar da hankali wajen wakoki amma zai rika yin fim jefi-jefi, musamman in an bukaci hakan.

4. Farfado da Kadawood.

Wani abun da kuma masu kallo zasu sa idon gani shine yadda za a farfado da Kadawood a jihar Kaduna.

Duk da kuwa Kadawood ta dade tana shirya fim amma basu samun karbuwa, amma suna ci gaba da kokari domin ganin hakarsu ta cimma ruwa.

5. Farfado da kasuwancin fim

Wannan shine abu da ya dade yana cin ma masana'antar tuwo a kwarya. Anyi taruka da dama, an hada kwamitoci da zummar ganin an shawo kan lamarin, amma hakan ya gagara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel