Kaico! Yaro dan shekara 14 ya mika kan sa ga masu garkuwa da mutane a Kaduna

Kaico! Yaro dan shekara 14 ya mika kan sa ga masu garkuwa da mutane a Kaduna

Wani karamin yaro mai shekaru 14 ya mika kan sag a gungun miyagu yan bindiga da suka yi awon gaba da mahaifiyarsa a unguwar Juji, Sabon Tasha, cikin karamar hukumar Chikun ta jahar Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yan bindigan sun shiga unguwar ne a ranar Talata suna harbe harben mai kan uwa da wabi suna shiga gidajen mutane suna dauke su, a haka suka shiga gidansu yaron suka dauke uwarsa, amma sai ya nemi su tafi da shi domin ba zai iya zama ba tare da mahaifiyarsa ba.

KU KARANTA: Kisan Janar Sulaiman: Trump ya bayyana burinsa na ganin ya sasanta da kasar Iran

Wani mazaunin unguwar ya bayyana cewa: “Da tsakar dare yan bindigan suka shigo Juji, kai tsaye suka dinga shiga gidajen jama’a suna bugu musu kofa wai su bude kofofinsu, amma da suka ji babu wanda ya amsa, sai suka fasa kofofin da tagogin.

“Da yake akwai karafa a cikin tagogin, sai suka yi amfani da diga wajen karya karafan, a haka suka ciro matar za su tafi da ita, amma sai yaronta ya roke su da su tafi da shi shima, yanzu tsawon sa’o’i 24 kenan basu tuntubi kowa ba.” Inji shi.

A wani labarin kuma, gungun yan bindiga sun kaddamar da hari a garin Beni dake cikin karamar hukumar Neja, inda suka yi awon gaba da babban limamin Masallacin Juma’an garin, Malam Umar Muhammad, tare da wasu mutane 20.

Rahotanni da dama sun bayyana cewa yan bindigan da yawansu ya kai 50 sun yi ta shiga kauyuka daban daban ne suka yi ma jama’a fashi, tare da kwashe shanunsu, daga nan suka afka Beni da Kudami na karamar hukumar Paikoro, a ranar Laraba.

Yan bindigan sun gamu da tirjiya a garin Kudami, amma basu samu wannan tirjiya a garin Beni ba, inda suka ci karensu babu babaka, suka fasa shaguna, gidaje, da kuma dauke musu babban limami yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa taron radin suna.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel