Siyasar 2023: Ina fatan Allah Ya min tsawon rai har Atiku ya zama shugaban kasa – Yahaya Kwande

Siyasar 2023: Ina fatan Allah Ya min tsawon rai har Atiku ya zama shugaban kasa – Yahaya Kwande

Guda daga cikin dattawan Arewa, kuma tsohon jakadan Najeriya a kasar Switzerland, Yahaya Kwande ya bayyana cewa duk ya kai shekara 90 a rayuwa, ba zai mutu ba har sai ya ga Atiku Abubakar ya zama shugaban kasar Najeriya.

Kwande ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da jaridar The Sun, inda yace a yanzu babu mutumin da Najeriya yake tsananin bukata ya jagoranceta a siyasance a matsayin shugaban kasa kamar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abunakar.

KU KARANTA: Kisan Janar Sulaiman: Trump ya bayyana burinsa na ganin ya sasanta da kasar Iran

Siyasar 2023: Ina fatan Allah Ya min tsawon rai har Atiku ya zama shugaban kasa – Yahaya Kwande
Yahaya Kwande
Asali: Facebook

A jawabinsa, Kwande yace a duk cikin masu gogoriyon takarar shugaban kasa daga jam’iyyu da bangarorin Najeriya, babu wanda ke da jama’an Atiku Abubakar, kuma babu wanda ya kai shi gogewa a harkar siyasa da iya tafiyar da mulki.

“Kai Atiku ya kai matsayin da a yanzu kamata ya yi mu je mu roke shi ya zo ya mulke mu, amma kasan yan Najeriya, sai dai ma wasu su fito suna yakarsa. Manya suna yi ma Atiku bakin cikin zama shugaban kasa ne saboda shi ba dan kowa bane.

“Ka san a yankin Arewa baka isa ka zama wani ba idan baka cikin wasu gungun manyan mutane, ko kuma mahaifinka ba daga cikinsu ya fito ba, don haka suke kallon Atiku wanda maraya ne ya girma Allah Ya daukaka shi a matsayin bare daga cikinsu.

“Amma Atiku mutum ne mai fikira, basira, sanin ya kamata, hangen nesa, kyauta, halasci kuma Allah Ya daukaka shi yau shi ne Wazirin Adamawa, kuma mutum ne mai kaunar jama’an sa, ka duba yadda ya kawo cigaba a harkar ilimi, kamfanin ruwansa, kamfanin taki da sauransu.” Inji shi.

Bugu da kari Dattijon ya nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka daga mukaminsa tun dai ya amsa cewa tsarin zaben daya kawo shi kan mulki na cike da kurakurai, har ma ya yarda cewa zai gyara kurakuran, don haka idan har da gaske yake ya sauka, sai a gyara.

Daga karshe Kwande yace: “Ka san cewa shekaruna 90, ka san dalilin da Allah Ya bani tsawon rai, Allah Ya bani aron tsawon rai ne domin na kasance cikin wadanda zasu jagoranci Atiku zuwa Villa, kuma ina ji a jikina ranar ta matso.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel