Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da babban limamin Masallacin Juma’a

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da babban limamin Masallacin Juma’a

Gungun yan bindiga sun kaddamar da hari a garin Beni dake cikin karamar hukumar Munya na jahar Neja, inda suka yi awon gaba da babban limamin Masallacin Juma’an garin, Malam Umar Muhammad.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito baya ga babban limami Malam Umar, yan bindigan sun tasa keyar wasu mutane 20 da suka tilasta musu tafiya dasu daga garin Beni.

KUKARANTA: Kisan Janar Sulaiman: Trump ya bayyana burinsa na ganin ya sasanta da kasar Iran

Rahotanni da dama sun bayyana cewa yan bindigan da yawansu ya kai 50 sun yi ta shiga kauyuka daban daban ne suna yi ma jama’a fashi, tare da kwashe shanunsu, daga nan suka afka Beni da Kudami na karamar hukumar Paikoro, a ranar Laraba.

Sai dai majiyar Legit.ng ta ruwaito yan bindigan sun gamu da tirjiya a garin Kudami, amma basu samu wannan tirjiya a garin Beni ba, inda suka ci karensu babu babaka, suka fasa shaguna, gidaje, da kuma dauke musu babban limami yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa taron radin suna.

Haka zalika yan bindigan sun kashe akalla mutane 4 a Beni da harbin bindiga, yayin da suka jikkata wasu da dama, wanda a yanzu haka an garzaya dasu babban asibitin Kafin Koro domin samun kulawa.

A wani labarin kuma, wasu gungun miyagu yan bindiga sun tattara wasu jami’an hukumar kwastam guda biyu, tare da yin awon gaba dasu a wani shingen binciken ababen hawa dake Dan-Bedi cikin karamar hukumar Jibia ta jahar Katsina.

Wasu mazauna garin sun tabbatar da cewa yan bindigan sun sace jami’an kwastam ne da safiyar ranar Laraba, 8 ga watan Janairu a kan hanyar Mallamawa Danbedi dake kan iyaka da kasar Najeriya da Nijar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel