Masu garkuwa sun yi awon gaba da jami’an kwastam 2 daga shingen binciken ababen hawa

Masu garkuwa sun yi awon gaba da jami’an kwastam 2 daga shingen binciken ababen hawa

Wasu gungun miyagu yan bindiga sun tattara wasu jami’an hukumar kwastam guda biyu, tare da yin awon gaba dasu a wani shingen binciken ababen hawa dake Dan-Bedi cikin karamar hukumar Jibia ta jahar Katsina.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito wasu mazauna garin sun tabbatar da cewa yan bindigan sun sace jami’an kwastam ne da safiyar ranar Laraba, 8 ga watan Janairu a kan hanyar Mallamawa Danbedi dake kan iyaka da kasar Najeriya da Nijar.

KU KARANTA: Kisan Janar Sulaiman: Trump ya bayyana burinsa na ganin ya sasanta da kasar Iran

Majiyar Legit.ng ta ruwaito ba jami’an kwastam din kadai yan bindigan suka sace ba, har da wasu ayarin matafiya dake kan hanyarsu ta zuwa Batsari daga garin Jibia, kamar yadda wani mazaunin garin ya bayyana.

Mazaunin garin, wanda ganau ne ba jiyau ba, ya bayyana cewa yan bindigan sun isa shingen binciken ababen hawan ne a kan babura da dama, inda suka kwace bindigun su, kuma ba tare da bata lokaci ba suka yi awon gaba dasu zuwa cikin dajin Rugu.

Kaakakin hukumar kwastam, Joseph Attah ya tabbatar da lamarin, inda ya bayyana cewa yan bindigan sun yi awon gaba da jami’in kwastam mai mukamin Inspekta da wani mai mukamin ‘Custom Assistant’.

Amma daga karshe, kaakaki Attah yace sun fara daukan duk wasu matakai da suka kamata don ganin sun ceto su tare da sauran matafiyan da yan bindigan suka yi garkuwa dasu.

A wani labarin kuma, gungun yan bindiga sun kaddamar da hari a garin Beni dake cikin karamar hukumar Neja, inda suka yi awon gaba da babban limamin Masallacin Juma’an garin, Malam Umar Muhammad, tare da tasa keyar wasu mutane 20.

Rahotanni da dama sun bayyana cewa yan bindigan da yawansu ya kai 50 sun yi ta shiga kauyuka daban daban ne suka yi ma jama’a fashi, tare da kwashe shanunsu, daga nan suka afka Beni da Kudami na karamar hukumar Paikoro, a ranar Laraba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng