Da duminsa: Sojoji sun kai mummunan hari sansanin 'yan bindiga a Katsina

Da duminsa: Sojoji sun kai mummunan hari sansanin 'yan bindiga a Katsina

Jami'an rundunar sojin Najeriya sun kai hari maboya da sansanin 'yan ta'adda dake dajin Jibia a jihar Katsina, in ji jaridar Daily Trust. Majiyoyi masu karfi sun tabbatar da cewa sun ji ruwan wuta kuma sun ga ababen hawa da jiragen sama na tafiya zuwa dajin.

A ranar Laraba ne garin Jibia ya fuskanci hare-haren sojin Najeriya wanda ya hautsina garin.

Mazauna sun bayyana cewa, sun ga wadanda suka samu raunika cikin sojin ana fitar dasu daga dajin ta hanyar amfani da ababen hawa kuma ana cigaba da fadan.

A lokacin da aka tuntubi mai magana da yawun runduna ta 17 din dake Katsina, Kaftin Kayode Owolabi, ya tabbatar da ruwan wutar da aka yi, yace an halaka 'yan bindiga masu yawa kuma sojoji sun samu raunika da dama.

DUBA WANNAN: Jami'an EFCC na can gidan Shehu Sani suna binciken kwakwaf

"A halin yanzu, ba zamu iya tabbatar da yawan 'yan bindigar da muka halaka ba, amma dai ba mu sassauta musu ba. Ba abun wasa bane gaskiya," in ji shi.

Ya ce, jami'an tsaron sun saka 'yan bindigar gaba. "Amma biyu daga cikin jami'anmu sun samu rauni. Mun halaka 'yan bindigar masu tarin yawa kuma har yanzu suna musayar wuta."

Ya musanta mutuwar wani babban soja da mazauna yankin suka fara yadawa, ya jaddada cewa jami'ai biyu ne kadai aka mika babban asibitin tarayya dake Katsina sakamakon raunin da suka samu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel