Guda daga cikin daliban da Kwankwaso ya baiwa tallafin karatu ya tallafa ma yara 150
Wani dalibi da ya ci gajiyar tsarin tallafin karatu kyauta na tsohon gwamnan jahar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Ibrahim Garba ya dauki nauyin karatun dalibai fiye da 150 a makarantun gaba da sakandari da dama a ciki da wajen Kano.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito Garba ya shiga cikin dalibai 501 da Kwankwaso ya turasu kasar Malaysia domin su yi karatun digiri na uku a bangaren dabarun tafiyar da kasuwanci, inda a yanzu haka yake koyarwa a sashin gudanar da kasuwanci na jami’ar Bayero.
KU KARANTA: Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Uwa da y’ayanta mata 3 sun mutu a gobara a Yobe
Garba yace ya dauki gabaran daukan tallafin daliban ne domin rage yawan yaran da basa zuwa makaranta, yace ya fara ne da dalibai 15 a shekarar 2019, inda zuwa yanzu ya dauki nauyin dalibai 30 a jami’o’in a Kano da makwabta jahohi.
Haka zalika ya dauki nauyin dalibai 40 a islamiyyu da kuma wasu dalibai 65 a makarantun Firamari. “muna duba dalibai ne masu kyakkyawan sakamako a WAEC, sai mu saya musu JAMB su zana, idan suka ci, sai mu nema musu gurabe a makarantun gaba da sakandari, mu cigaba da daukan nauyinsu har su gama.
“A shekarar da ta gabata mun dauki nauyin dalibai 15, a bana ma mun dauki sabbi guda 15, muna fatan zamu cigaba da kara adadin daliban dake cin gajiyan tsarin, ban san iyayen yawancin daliban ba, kawai dai muna duba cancanta ne.” Inji shi.
Ibrahim yace yana fatan cigaba da daukan nauyin dalibai kamar yadda Kwankwaso ya yi masa, don haka ya bayyana godiyarsa ga tsohon gwamnan daya kirkiro wannan tsari, sa’annan ya yi kira ga Kwankwaso ya cigaba da wannan aikin alheri har sai sun rage jahilci a Kano.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng