A kalla mutane 11 sun mutu a wani hatsarin mota a Kano

A kalla mutane 11 sun mutu a wani hatsarin mota a Kano

A kalla mutane 11 ne rahotanni suka bayyana cewa sun rasa ransu a wani hatsarin mota da ya faru a Kano ranar Laraba.

Jaridar The Nation ta rawaito cewa shaidar gani da ido ya sanar da ita cewa hatsarin ya afku ne a kauyen Tsaida dake daf da karamar hukumar Gaya.

Shaidar ya sanar da cewa an dauki gawar wadanda suka mutu zuwa babban asibitin karamar hukumar Gaya.

"Hatsarin mota ne da ya ritsa da motoci guda uku; wata motar fasinja da wasu motoci guda biyu," a cewar shaidar.

Hatsarin ya faru ne da misalin karfe 11:00 na safiyar ranar Laraba.

DUBA WANNAN: Sayen tsohon layin waya da diyar Buhari, Hanan, ta taba amfani da shi ya jawo wa matashi daurin watanni

A ranar Talata ne aka binne gawar Malam Sagir Madaki, darektan hukumar kwana -kwana ta jihar Kano, a makarbatar Dandolo dake unguwar Goron Dutse a yankin karamar hukumar Gwale.

Jaridar Solabase dake Kano ta rawaito cewa wani dan uwa ga marigayin mai suna Ibrahim Umar ya ce Malam Sagir Madaki ya mutu ne da yammacin ranar Talata a asibitin koyarwa na Aminu Kano bayan takaitacciyar rashin lafiya.

An yi masa sallar jana'iza bisa tsarin addinin Musulunci a unguwar Yola dake cikin birnin Kano, a yammacin ranar Talata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel