Yan bindiga sun amshe wani gari a Neja, sun fatattaki mutum 2,500

Yan bindiga sun amshe wani gari a Neja, sun fatattaki mutum 2,500

Rahotanni sun kawo cewa an tursasa wa sama da mutane 2,500 a garuruwa daban-daban da ke karamar hukumar Munya na jihar Niger barin gidajensu sakamakon hare-haren yan bindiga.

Lamarin ya kara munana ne da harin ranar Lahadi da yan bindigan suka daukaka, wanda ya yi sanadiyar mutuwar wani babban soja da wasu sojoji uku.

An tattaro cewa yan bindigan sun amshe garin Kabuka sannan sun mayar dashi sansanin aikinsu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mutanen da aka fatattaka wadanda mafi akasarinsu mata ne na daukar mafaka a wani makarantar Firamare da ke Sarkin Pawa a hedkwatar karamar hukumar.

Sauran garuruwan da abun ya shafa sune Ingu Kasa, Anguwan Bussa, Galuwi, Almujere, Toko, Anguwan Zarumai da Anguwan Kwata.

Hare-haren ya kuma shafi garuruwan Katarma da Kuduru a karamar hukumar Chikun da ke jihar Kaduna, wacce ke raba iyalan da jihar Niger. Mazauna garuruwan biyu na sun samu mafaka a wasu yankunan jihar Niger.

KU KARANTA KUMA: Sojoji sun mayar wa Gwamna Zulum martani kan zargin da yayi musu

A halin yanzu, gwamnatin jihar Niger ta tura karin jami’an tsaro a garuruwan da abun ya shafa, wadanda tuni sun bi sahun yan bindigan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: