Tirkashi: Hankalin mutane ya tashi a kasar China bayan sun wayi gari sun ga rana guda 3 ta fito

Tirkashi: Hankalin mutane ya tashi a kasar China bayan sun wayi gari sun ga rana guda 3 ta fito

- Mazauna babban birnin Fuyu na kasar China sun matukar girgiza da ganin kwallayen rana uku sun fito

- Kwallayen ranar sun dinga matukar haske a sararin samaniya har na wajen mintuna 20 kafin su bace

- Wannan lamarin ko karin kwallayen ranar ana kiransu da "sun dog"

Mazauna babban birnin Fuyu na China sun sha matukar mamaki da al'ajabin abinda ya faru a makon nan. Kamar yadda aka saba dai, rana daya ce ke fitowa sannan ta fadi, amma ba hakan bane ya faru a makon. Rana uku ne suka bayyana kuma suka dinga haskawa, abun cike da mamaki.

Wasu manyan kwallayen haske suka bayyana a kowanne gefe na rana, hakan kuwa ya disashe hasken ranar don sune suka dinga haskawa.

Wannan lamarin ya faru ne a ranar karshe ta shekarar 2019 a yankin Jilin dake Arewa maso gabas na kasar.

Kamar yadda CGTN suka bayyana, rana uku sun bayyana a sararin samaniya a arewa maso gabas na China.

KU KARANTA: Tirkashi: Sojoji mata sun nuna damuwarsu kan rashin samari masu zuwa neman aurensu

Wannan ne ake kira da "sun dog" ko kuma rana ta wasa. An gano cewa, wadannan karin ranar guda biyu manyan kwallayen kankara ne kuma hasken ranar ne ke basu wannan tsananin hasken da suke dashi.

Wannan kwallayen ranar sun yi dadewar mintuna 20 a sararin samaniya kafin su bace.

Abun mamakin da wadanda basu fahimci lamarin ba suka dinga yi shine, duba da tsananin haske da kuma zafin da rana ke samarwa, ya duniya zata kasance idan kamarta guda biyu suka karu?

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng