Tirkashi: Sojoji mata sun nuna damuwarsu kan rashin samari masu zuwa neman aurensu

Tirkashi: Sojoji mata sun nuna damuwarsu kan rashin samari masu zuwa neman aurensu

- Ga maza masu tarin yawa a Najeriya, akwai matukar wahala su tunkari mace soja da soyayya

- Wasu mata sojoji biyu na Najeriya, sun koka da yadda ba a kawo musu tayin soyayya kwata-kwata

- Mutane da yawa kuwa sun bayyana cewa, bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane

Ga maza masu tarin yawa a Najeriya, akwai matukar wuya a ga sun tunkari mace ma'aikaciya a rundunar sojin Najeriya da maganar soyayya.

Komai kyan mace kuwa da sakin fuskarta, in har soja ce, akwai yuwuwar masu neman aurenta su zama soja dan uwanta.

Hakan ce kuwa ta faru da wasu sojojin Najeriya kuma mata guda biyu.

Sun garzaya shafukansu a kafar sada zumuntar zamani inda suke kira ga mazan dake musu kallon soyayya da kada suyi kasa a guiwa. Su hanzarta zuwa neman aurensu tare da dena jin tsoronsu. Sun kuma yi kira ga jama'a da su dena kallon matsayinsu na sojoji.

KU KARANTA: Da duminsa: Jirgin sama yayi hadari dauke da mutane 180 a kasar Iran

Ga abinda suka rubuta: "Ba laifi bane don an so mutum. Babu wanda zai daka masoyinshi. Ku harba kurciyarku don mu ma mutane ne kamar ku. Ku kawo mana tayin soyayyarku."

Wannan lamarin kuwa ya jawo cece-kuce don wasu sun ga gaskiyar sojojin tare da basu karfin guiwa. A bangaren wasu kuwa, sun bayyana cewa su fa babu yadda za a yi su tunkari sojoji da tayin soyayya, duk da yadda mata ke da yawa a gari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel