Da duminsa: Jirgin sama yayi hadari dauke da mutane 180 a kasar Iran

Da duminsa: Jirgin sama yayi hadari dauke da mutane 180 a kasar Iran

- Wani jirgin saman kasar Ukraine ya tarwatse a kasar Iran

- Ana zargin dukkan fasinjoji 180 tare da matukan jirgin sun rasa rayukansu

- An gano cewa, jirgin ya watse ne jim kadan bayan da ya nufi filin jiragen sama na Boryspil dake Kyiv a kasar Ukraine

Wani jirgin saman kasar Ukraine ya yi hatsari a Iran. Dukkan fasinjoji 180 tare da matukan jirgin farar hular sun rasa rayukansu, kamar yadda Red Crescent na kasar Iran suka sanar.

Aljazeera ta bayyana cewa, kafar yadar labaran ta Iran tace jirgin mai lamba 737-800 ya fadi kusa da Parand, wani yanki na kudu maso yamma na babban birnin Tehran jim kadan bayan da ya tashi.

Faduwar jirgin ya auku ne sa'o'i kadan bayan da Iran ta kai hari ga rundunar sojin Amurka don mayar da martani a kan kisan kwamanda Soleimani da Amurka tayi.

An gano cewa jirgin ya doshi babban filin tashi da saukar jiragen sama ne na Boryspil dake birnin Kyiv na kasar Ukraine.

KU KARANTA: Sai dana sha kukana na more lokacin da aka biya ni albashina na farko a kasar Saudiyya - Likita dan Najeriya

"Wata kungiyar bincike da bangaren kula da sufurin jiragen sama na kasar ta tura inda lamarin ya faru, sune suka bayyana labarin abinda ya faru.

"Zamu bada cikakken bayani a takarda ta gaba," cewar kakakin kungiyar da bangaren sufurin jiragen sama ta Iran ta tura, Reza Jafarzadeh. Ya sanar wa da manema labarai hakan ne a Tehran.

Asalin kamfanin jirgin saman ya ce, yana sane da rahoton kafafen yada labarai kuma yana tattara bayanai ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel